Bauchi ta inganta rayuwar jama’arta -In ji Baba Tela

Baba Tela
Jamilu Barau daga Bauchi
Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir na jihar Bauchi ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar cibiyar nazarin dabarun siyasa ta kasa reshen jihar Filato a wata ziyarar ban girma da suka kai ranar Litinin a ofishinsa.
Gwamnan jihar Bauchi wanda mataimakinsa, Sanata Baba Tela ya wakilta ya shaidawa mahalarta taron cewa, gwamnati mai ci ta gina cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko na fiye da 300 a fadin jihar, da amincewar kananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu da sauran ayyukan raya kasa domin inganta rayuwar jama’a.
Ya ce, cibiyar manufofin tana taka muhimmiyar rawa wajen bullo da manufofin da suka shafi al’umma kai tsaye musamman a matakin kananan hukumomi. Domin haka gwamnan ya yaba wa tawagar bisa ziyarar bisa alkawarin da gwamnatin jihar ta bayar akan hakan.
Da yake jawabi, shugaban tawagar, Dokta Ibrahim Choji ya ce, sun je ofishin gwamna ne domin yi masa bayani kan ayyukan da gwamnatin tarayya ta dora masu.
A cewarsa, ayyukansu sun hada da tarurrukan karawa juna sani, laccoci da yin tambari da zurfafa bincike kan al’amuran da suka shafi al’ummomin yankin. Dokta Ibrahim Choji ya ce, ayyukan cibiyar nazarin dabarun siyasa ta kasa sun hada da tsara manufofi ga shugabannin gwamnati da masu zaman kansu, hafsoshin soja da matsakaita da manyan ma’aikatan gwamnati.
Ya ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da cibiyar da ta gabatar da rahotonta kan batutuwan da aka zaba na tsawon watanni 10 tare da neman gwamnatin jihar goyon baya domin cim ma burinta, gwamnatin ta ce, tana aiki ba dare ba rana domin inBaba Tela ganta rayuwar al’umma daga tushe.
Gwamnan jihar, Sanata Bala Muhammad ya bayyana haka a lokacin da ya karbi Daga Mahmud Gambo Sani A yau Juma’a, majalisar sarakunan samarin Nijeriya, karkashin jagorancin Mai martaba sarkin samarin Nijeriya, Alhaji Sani Uba ke bikin nadin Dokta Abdullahi Idris Muhammad, shugaban cibiyar bayar da magungunan gargajiya ta Danfodiyo, a matsayin Jakadan Matasan Nijeriya.
Toron wanda za a gudanar a Gidan Dan Hausa da ke titin Sakkwato a birnin Kano, ana sa ran halartar iyayen taro wadanda suka hada da Masu martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero da sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya da sarkin Rano, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa da kuma sarkin Karaye, Alhaji Ibrahim Abubakar. Ina sa ran taron zai sami halartar manyan mutane daga cikin jihar Kano da wajenta domin taya shugaban cibiyar ta Danfodiyo murnar samun sarautar.
A yau ake nadin Danfodiyo Jakadan Matasan Nijeriya bakuncin tawagar cibiyar nazarin dabarun siyasa ta kasa reshen Kuru Jos Filato a ziyarar ban girma da suka kai ofishinsa.