Bauchi za ta yi aiki da bankuna -Wajen bunkasa tattalin arziki

Idan masalaha ta gagara, ba na tsoron bugawa da kowa -Bala Mohammed

Bala Mohammed

Tura wannan Sakon

Jamilu Barau daga Bauchi

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar Bauchi ya ce, gwamnatinsa ta kulla kyakkyawar alaka da bankuna da hada-hadar kudi domin bunkasar tattalin arzikin jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da shugabannin cibiyar ma’aikatan banki ta Nijeriya (Charted Institute of Bankers of Nigeria) suka kai masa ziyarar bayar da shawara a zauren majalisar da ke gidan gwamnati.

Gwamna Bala ya bayyana cibiyar a matsayin babbar mai ruwa da tsaki a harkokin kudi tare da neman goyon bayansu domin bai wa gwamnatin jihar damar samun karin kudaden shiga.

“Na yi matukar farin cikin tarbar ku domin yin cudanya da juna, ina sane da kokarin da cibiyar ma’aikatan banki ta Nijeriya take yi na kare muradun tsarin bankunan Nijeriya.”

“A madadin gwamnati da al’ummar jihar Bauchi ina jinjina wa cibiyar na gina dakunan karatu a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa Bauchi domin amfanar daliban banki da kudi” in ji shi.

Gwamnan ya ce, gwamnatin jihar za ta ci gaba da hada hannu da hukumomin kudi da masu ruwa da tsaki domin bai wa gwamnatinsa kyakkyawan shugabanci. A nasa bangaren, shugaban cibiyar, Dokta Bayo Olugbemi, ya ce, cibiyar ta kasance a Bauchi domin hada kan masu ruwa da tsaki da harkokin banki da nufin tabbatar da ci gaba da bunkasa fannin banki da kudi a jihar.

“Cibiyar ta yaba wa gwamnatin jihar Bauchi bisa tallafin da take bai wa bankuna ta hanyar samar da ingantaccen tsarin tsaro wanda ya samar da yanayi mai kyau ga harkar bankuna da hada-hadar kudi a jihar.” in ji shi.

Daga karshe, shugaban ya shaida wa gwamnan cewa, cibiyar ta fara gina dakin karatu na zamani mai dauke da mutane 160 a kokarinta na zurfafa nazarin harkokin bankuna da hada-hadar kudi ta yadda za a magance gibin da ke tsakanin masana’antu da masana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *