Bayan da ya yi ritaya: Kwamishinan ‘yan-sandan Kano bai yi nadama ba

kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, Sama’ila Shu’aibu Dikko,

kwamishinan ’yan sanda Sama’ila Dikko

Tura wannan Sakon

Daga Rabiu Sunusi Kano

Tsohon kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya bayyana cewa, ba ya danasanin zama dan sanda a rayuwarsa, do­min aiki ne mai cike da tarin lada da taimkon al’umma, da kuma kare hakkin bil’adama.

Tsohon kwamishinan ya bayyana haka, a yayin da yake ban kwana da rundunar ’yan san­da a jihar Kano, wanda ya kawo karshen lokacin aikinsa na cika shekaru 60 da haihuwa. Ya ce, babu abin da zai ce wa al’ummar Kano sai godiya bisa yadda ya sami goyon baya yayin da yake shugaban rundunar ’yan sanda ta jihar.

Dikko ya kara da cewa, loka­cin da ya zo a matsayin shugaba a hukumar sai da yafara kai zi­yara ga kowace hukuma da take gudanar da tsaro, domin samun fahimtar yadda za a kara samar da tsaro a jihar Kano.

Dikko, wanda shi ne kwamishinan ’yan sanda na 42 a jihar Kano, ya yi aiki na tsawon watanni 17 a matsayin shugaban ’yan sanda a jihar, ya yi matukar godiya ga Allah madaukakin Sar­ki da ya ba shi damar zama shug­aban rundunar a Kano, tare da samun dumbin nasarori dakuma kammala aikin cikin nasara.

Ya kuma nuna godiyarsa ga shugaban rundunar ’yan sanda ta kasa, Usman Alkali Baba, bisa sahilewar da ya yi masa na zama kwamishinan ’yan sanda a jihar Kano, da kuma ba shi dama do­min gudanar da aiki tare da samar wa rundunar kayan aiki da sauran abubuwan da suke bukata domin kawo karshen marasa son zaman lafiya a kasa.

Bayan wannan, ya jinjina da yin fatan alkhairi ga masarautun jihar tare da sarakuna guda biyar bisa gudunmuwar da suke bai wa hukumar wajen gudanar da aikin­ta, inda ya kara bukatar samun goyon bayansu ga duk wanda zai zo a matsayin wanda zai canje shi.

Ya kuma nuna godiyarsa da fatan alkhairi ga shugabanin ’yan kasuwa da sauran kungiyoyin da suke fadi wajen tsabtace matsalo­lin da ke addabar jihar.

Ya gode wa gwamnatin jihar Kano bisa bai wa rundunar hadin kai da goyon baya, bisa tsabtace jihar daga miyagu, musamman gyaren ababen hawa da gwamna­tin ya yi da kuma wadanda huku­mar Karota ta samar wa rundunar da kuma sauran hukumomin jihar.

Haka zalika, ya gode wa ma­taimakin shugaban rundunar ’yan sanda na kasa, mai kula da shiyar Kano, da ma wanda ya karb i ku­jerar ta kwamishinan ’yan sanda a hannunsa bisa sa shi a kan hanya da suka yi, wanda hakan ya ba shi damar samun nasarar da ake kallo a halin yanzu, da kuma aiki tuk­uru da ya gabatar.

Ya kuma bayyana tsarin tura jami’ansu lungu da sako na jihar domin dakile dukkan wasu da ke tunanin aikata laifi, a matsa­yin tsarin day a yi nasara, ganin jami’an tsaron zai sa masu aikata laifi su ji tsoron aikatawa.

Haka kuma, batun kai sumame, Dikkoya ce, tsarin ya ba su nasara matukar gaske a lokutan ayyu­kansu, kasancewar duk inda suka sami bayanan sirri za su kai dau­ki, sannan samar da ofishin Anti Daba da sauran b angarori da hu­kumar ta samar domin magance ta’addanci adalcin a Kano, sun haifar da da mai ido.

“Kusan dawannan nake kallon ba na da na sanin zama dan san­da a rayuwata, domin taimakon al’umma da ma kasata Nijeriya.” A cewar Dikko.

Bayan jawabai daga bakin al’ummomi daban daban da suka gabata, rundunar ta karrama wasu masu ruwa-da-tsaki da wasu daga cikin jami’an hukumar da suka yi kwazo wajen aikinsu.

Rundunar ta kuma karrama wasu daga cikin gidajen jaridu da ma shugaban kungiyar ’yan jari­da na jihar Kano, kwamared Ab­bas Ibrahim da sauran ’yan jarida tare da jami’in hurda da jama’a na rundunar, SP Abdullah Haru­na Kiyawa, bisa kokarin da yake na wayar da kan al’ummar jihar Kano ta kowace fuska a b angaren tsaro.

Bayan karrama wadannan b angarori, shi ma kwamishi­nan ’yan sandan, mai ritaya CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya sami lambobin girmamawa daga b an­garori mabambanta yayin taron, bisa namijin kokarinsa a lokacin aikinsa a matsayin kwamishinan ’yan sandan jihar.

Daga karshe, an yi masa fatan alkhairi tare da bukatar ya ci gaba da zama a jihar Kano domin gu­danar da al’amuransa na yau da kullum, inda ya ce, zai zauna da sauran ’yan uwa da abokan arziki tare da shawarar abin da yaka­mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *