Bayan kaddamar da hako man fetur a Arewa: Shugaba Buhari ya yi hasashen zuba jarin biliyoyi

Daga Aliyu Umar
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana kyautata zato kan sanya jari na dalar Amirka biliyan uku cikin harkar hako man fetur da iskar gas da aka gano a Kolmani, tsakanin jihohin Bauchi da Gwambe.
Da yake gabatar da jawabinsa a wajen bikin kaddamar da aikin fara hako man fetur na farko a Arewa,a ranar Talatar da ta gabata,shugaba Buhari ya ce, aikin zai kunshi tace iskar gas da danyen man fetur da karfin hasken lantarki da kuma takin zamani.
Ya ce,la’akari da fadin murabba’in kasar da man ke kwance jingim da kuma tsananin bukatar sanya jari da tattalin arzikin kasa, abin na cike da kalubale,inda ya bukaci hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa( NNPC) da ta tabbatar da daidaita al’amuranta, ciki da waje. Shugaban ya kuma bayyana cewa, gwamnatinsa ta ja damarar ganin aikin ya janyo saka jari na fiye da dalar Amirka na fiye biliyan 3.
Daga nan, ya jinjina wa hukumar kula da albarkatun man fetur ta Nijeriya saboda tabbatar da gano danyen man fetur da iskar gas filin kogin Kolmani
Inda ya yi hasashen cewa, man zai kai ga bunkasa masana’antu a Nijeriya da karin karfin hasken lantarki,nan da shekara ta 2060.
Sauran wadanda suka gabatar da jawaban fatan alheri,sun hada da gwamnonin Bauchi da Gwambe,Bala Mohammed da Muhammad Inuwa Yahaya,bi da bi,da shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Mista Simon Lalong da shugaban majalisar dattijai, Dokta Ahmad Lawan da kuma dan takarar shugabancin kasa na APC, Jagaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.