Bayan tashin-tashina, kura ta lafa a birni Jos -Gwamnati

Gwamna Lalong
Gwamnatin jihar Filato, ta sanar da cewa, jami’an tsaro sun yi nasarar mayar da doka da oda a yankin Gada Biyu dake birnin Jos sakamakon tashin hankalin da aka samu ranar Litinin da ta gabata wanda ya haifar da kone-kone da kuma harbe-harben bindiga.
Wannan ya biyo bayan abin da ake dangantawa da yunkurin dau
kar fansa da wadansu matasa suka yi sakamakon harin da aka kai karamar hukumar Bassa da ake zargin makiyaya a kan ‘yan kabilar Irigwe abind a ya yi sanadiyar rasa rayuka da kuma kona gidaje.
Harin na zuwa ne kwanakin bayan wani irinsa da aka kai karamar hukumar Riyom abin da ya sa majalisar tsaron jihar ta gudanar da taron gaggawa, inda aka bai wa sojoji umurnin kara yawan jami’an su a yankunan kananan hukumomin da ake samun tashin hankalin.
Sanarwar da Daraktan yada labaran gwamnatin jihar, Dokta Makut Simon Macham ya rarraba wa manema labarai ta tabbatar da tura jami’an tsaron da kuma kwantar da tarzomar.
Macham ya ce, matakin ya biyo bayan harin da aka kai wa wadansu motoci guda biyu da kuma cinna masu wuta lokacin da matasa suka tare babbar hanyar Gada Biyu.
Gwamnatin jihar ta gargadi jama’ar jihar da su kauce wa daukar doka a hannunsu wajen tare hanya suna kai hari a kan matafiya.