Bayero za ta mayar da litattafan Ibrahim Yaro kundi –Farfesa AZare

Tura wannan Sakon

Daga Muhammadu Mujittaba Bin Usman Kano

Cibiyar binciken harsuna Nijeriya da Fassara da hikimomin al’umma ta jami’ar Bayaro, da ke Kano karkashin shugabancin Farfesa Yakubu Azare ta sha alwashin mai da sa wadansu littafin tatsuniyoyin da wasanni da sauran litatafi na hikima da fasaha da Marigayi Ibirahim Yaro Yahaya ya rubuta kundi domin amfanin yaranmu su rinka kallo a telebinjin da sauran kafofin sadarwa na zamani ta yadda katun mai dauke hotuna da sauti da sauran su kuma a harshen Hausa.

Wanda yara za su kalla maimakon kallon katon din da ba namu ba, kamar na Tom da Jerry wanda ba na harshen mu ba ne kuma bana al’adar mu ba ne, amma wannan zai yi daidai da harshen mu da al’adunmu, da tarbiyarmu da wadanna litattafi na Marigayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya, suka taka rawa wajen yada ililmi da tarbiyarmu.

Kamar yadda ni na ci gajiyar Marigayi Ibrahim Yaro Yahaya, wajen samu tarbiyya da taimako a kan harkar rayuwa da ilimi nan ta sanadiyyar halayansa nagari da jama’a na kusa da na nesa suka san shi a kai.

Bayanin hakan ya fito daga bakin Farfesa Yakubu Azare, shugaban cibiyar binciken harsunan Nijeriya da fassara da hikimomin al’umma, ta jami’ar Bayaro da ke Kano, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a jami`ar Bayero ta kano, In dai za a iya tunawa a watanin baya ne aka yi taron tunawa da irin gudumawar da Marigayi Ibrahim Yaro Yahaya da ya bayar ga harshen Hausa, wanda ya sa muka halatar manyman masana harshan Hausa da sauran masana a fannununi da dama an yi shi ne karkashin shugabancin tsohonmataimaki shugaban jami’ar Bayaro, Farfesa Sani Zaharideen kuma baban limamin Kano sai kuma manya baki masu jawabi wanda suka hada da Emarutus Abdulkadir Danganbo, da Emarutus Dan Datti, haka kuma akwai Farfesa Abdallah Uba, Farfesa Gusau, Farfesa Baban zara, sai kuma Alhaji Ahamad Gesto Kwararen Kuma Fitacen Ma’aikacin Rediyo, Daya daga cikin wanda suka shugabanci FRCN Kaduna, da dai sauran dimbin masana da suka bayana tarihi da nagarta, hakuri da juriya ta margayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya.

A karshe, Alhaji Muhammad Nasiru Ibrahim Yaro Yahaya, wanda da ne ga Marigayi Yaro Yahaya, yaba wa cibiyar buciken harsuna ta Bayaro ya yi da daukacin shugabanin da abokai da makusanta da dalibai da sauran jama’a da suka shirya taron karrama mahaifinsu da cewa, alamace ta cewa, sunriki zumunci da taimako da tarbiyyar mu har yanzu ba su bar mu suna tari da mu cikin farin ciki ko akasin haka dan haka muna yaba masu da kuma addu’ar Allah ya biya su abin da suke yi wa iyalan Marigayin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *