Borno ta amince da kaddamar da shirin ruga

Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
Gwamnatin jihar Borno ta amince da kaddamar da shirin nan na gwamnatin tarayya, domin makiyaya Ruga da zimmar zaunar da makiyayan da rikicin Boko Haram ya shafa da suka rasa wuraren kiwo.
Shiri na gwamnatin Borno domin makiyaya a cewar gwamnatin za a samar da shi ne a yankuna uku a fadin jihar, da sunan hada da garuruwan Mafa, Gubio da kuma Rumirgo cikin karamar hukumar Askira/Uba.
Kamar yadda tsarin yake wannan shiri na Ruga shiri ne da gwamnatin tarayya ta aminta da shi tare da bayar da goyon baya a kansa wanda ta ware fiye da Naira biliyan 4 domin gudanar da shi cikin shekaru 25 bisa tsari. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Kodinetan shirin aa jihar Borno, Dokta Osman El-Fal a cibiyar Rug da ke Mafa kan hanyar Dikwa.
A cewar kodinetan, shirin Ruga ya lakume fiye da Hekta 250 wanda ya kunshi kayayyaki daban-daban ciki da ya kunshi fiye da gidaje 100 domin sake zaunar da makiyayan a yankin Mafa. Sauran abubuwan da aka samar a cibiyar makiyaya sun hada da makarantar firamare da kuma wani karamin asibitin kula da dabbobin makiyayan.
A cewar Kodinetan baya ga shiri har wa yau za a samar musu da wadansu sababbin hanyoyi domin yin noma ga makiyaya musamman noman kayayyakin abinci hade da abincin dabbobi.
Har ila yau, za a gina madatsun ruwa guda 3 domin makiyaya su samu wuraren shayar da dabbobin su da kuma samun damar noman kayayyakin marmari da na miya kana su kuma matan makiyayan za a horar da su a kan kiwon kifi da kiwon kaji da koyon dinki.
Ya kara da cewa, baya ga haka kuma gwamnatin jihar za ta gabatarwa makiyayan hanyoyin zamani domin bi wajen samar inganta nono da madara a wadace sabanin yadda yake a gargajiyance.
Tijjani Mohammed ya kara da cewa, gwamnatin za ta samar da irin shanu guda 100 da za a bai wa makiyayan tare da samar da wadansu iri daban-daban guda 75 da ake da su a yankin Sakkwato da ake yi wa lakabi da Gudali da ke iya jure zafin yanayi irin na wannan yanki na Borno.
Ya bayyana cewa, shirin Ruga shiri ne da aka samar da shi musamman duba da yadda harkokin tsaro suka samu koma baya kana wannan tsari zai sanya yankin ya zama cibiyar samar da madara da nono yadda hatta mutane daga babban birnin jihar Maiduguri za su rika tururuwa domin zuwa sayen nono da madara.
Da ya ke mayar da martani Dokta El-Fal ya ce, duk da cewa, shi ba makiyayi ba ne amma kuma ya yaba matuka bisa yadda aka tsara shirin jihar Borno, Tijjani Mohammed yayin da yake bayanin hakan ga wadansu wakilin kasar Sudan kan tattalin arziki.