Buhari, Osinbajo sun yi allurar riga-kafin Korona

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Sahugaban kasa Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Yemi Osinbajo sun karbi alluran farko ta riga-kafin Korona ta kamfanin AstraZeneca.

Riga-kafin wanda aka nuna kai-tsaye a tashoshin talbijin, kwana guda bayan fara shirin riga-kafin na kasa da aka fara yi wa ma’aikatan kiwon lafiya da ma’aikatan babban Asibitin Kasa da ke Abuja.

Bayan da aka yi masa allurar, shugaba Buhari ya ce “Na karbi allurata ta farko kuma ina so na yaba wa duk ‘yan Nijeriya da suka cancanta, su yi hakan domin a kare mu daga kwayar cutar,” kamar yadda wata sanarwa daga fadar ta bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *