Buhari, shugaba mafi talauci a Afirka

Buhari, shugaba mafi talauci a Afirka
Shugaba Buhari ya sake zamowa shugaban da ya fi kowane shugaba talauci a Afirka.
Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya, a wannan shekarar ta 2021 shi ne shugaban da ya fi kowane shugaba talauci a Afirka.
Kamar yadda mujallar Forbes da ke Washington ta bayyana, cikin shekaru fiye da shida da shugaban ya kwashe yana mulkin Nijeriya, adadin kudaden da ya mallaka a lalitarsa su ne DalarAmirka 150,000, kwatankwacin Naira miliyan 30 kudin Nijeriya.
Sai gidaje biyar da kuma wadansu gidaje biyu na qasa, daya a mahaifarsa da ke Daura sannan daya a Katsina.
Sai kuma garken shanu guda 270, tumakai 25 , dawakai biyar da kuma gonar noma.
Haqiqa duk da kasancewa shugaban yana da wadansu kura-kurai a mulkinsa, amma ya sha bamban da sauran shugabannin qasa wadanda suka wawure dukiyar qasar suka arzurta kawunansu da ‘ya’yansu.