Buhari ya hasaso yakin basasa, muddin…

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gargadi ’yan Nijeriya cewa, da kada su yarda a sake samun barkewar yakin basasa irin na shekarar 1967 zuwa 1970.
Ya furta kalaman ne a daidai lokacin da ake samun baraka tsakanin al’ummar kasar dangane da abubuwan da suka shafi siyasa.
Shugaba Buhari ya ce, son rai ne babban dalilin da ya haddasa yakin da ya lakume rayukan miliyoyin ‘yan Nijeriya, sai dai ya jaddada cewa, Nijeriya za ta ci gaba da zama kasa daya dunkulalliya.
A lokacin da ya ke ganawa da tsofaffin shugabannin rusasshiyar jam’iyyar CPC, ya ce, an samar da jam’iyar ne bisa kishin kasa da kuma biyayya ga hadin kan Nijeriya.
Shugaban ya bukaci dukkanin ‘yan rusasshiyar jam’iyyar da sauran jagororin siyasa da a kodayaushe su mayar da hankali wajen samar da hadin kai da zaman lafiya da kuma kimar kasar.
Buhari ya yi la’akari da kudurin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, wanda ya haifar da samar da jam’iyyar bai gurgunce ba, domin haka ya bukaci ‘yan kasar da su kara jajircewa.