Buhari ya ja damarar kawo karshen zazzabin cizon sauro

Muhammadu Buhari

Muhammadu Buhari

Tura wannan Sakon

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a fadar shugabancin kasar da ke Abuja.

Ana sa ran kwamitin zai aiwatar da kudurin gwamnatin tarayya na kawo karshen zazzabin cizon sauro a kasar. Da yake jawabi ga majalisar mai wakilai 16 a karkashin jagorancin shugaban rukunin Dangote Aliko Dangote wanda ya amince da zama jakadan yaki da cutar zazzabin cizon sauro.

Shugaban ya ci gaba da cewa, gwamnatinsa za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen yaki da zazzabin cizon sauro a fadin kasar. Rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya na 2021, ya nuna cewa, Nijeriya ce kadai ke da kashi 27 cikin 100 cikin kasashen da ke fama da cutar zazzabin cizon sauron, a yayin da mace-macen mata masu juna biyu ke da kashi 32 cikin 100.

Cutar zazzabin cizon sauro na iya haifar da cututtuka masu tsanani da rikitarwa ga mata masu juna biyu kuma yana haifar da yawan zubewar ciki, yayin da cutar ke kashe jarirai da yara kanana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *