Buhari ya yi alwashin saukar da farashin shinkafa

Buhari ya yi alwashin saukar da farashin shinkafa

Buhari ya kadamar da dalan shinkafa

Tura wannan Sakon

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yiwuwar farashin shinkafa ya sauka a kasuwanni bayan kaddamar da Dalar shinkafa har 13 karkashin shirin tallafa wa manoma domin ciyar da kasa bisa jagorancin bankin CBN. A ranar Talatar

da ta gabata, shugaba Buhari ya jagoranci kaddamar da dalar shinkafar, inda ya ce, gwamnatinsa na daukar dukkan matakan da suka dace domin saukaka farashin kayayyaki musamman na abinci da shinkafar a kan gaba.

Farashin shinkafa ya yi tashin gwauron zabi a fadin kasar bayan matakin gwamnati na kulle iyakokinta da makwabta a shekarar 2019 ciki har da iyakar Seme da ta hada ta da Jamhuriyyar Benin.

A wancan lokaci dai gwamnati ta ce, matakin kulle iyakar wani yunkuri ne na hana fasakwabrin kayayyaki da kuma karfafa gwiwar manoman cikin gida.

Bayanai sun ce dalar 13 an samar da duk guda daya daga gonakin shinkafa miliyan 1 da aka yi aikin noman ta a sassan kasar a karkashin shirin tallafa wa manoma na ABP da shugaba Buhari ya kaddamar a shekara ta 2015 wanda babban bankin (CBN) ya jagoranta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *