Buhari ya yi waje da ministoci 2

Buhari ya yi waje da ministoci 2

Buhari ya yi waje da ministoci 2

Tura wannan Sakon

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kori ministocinsa guda biyu da suka hada da ministan noma, Alhaji Sabo Nanono da takwaransa na hasken lantarki Saleh Mamman.

Mai magana da yawun shugaban, Femi Adeshina ya tabbatar da korar manyan jami’an guda biyu wadanda ke rike da manyan ma’aikatu a karkashin gwamnatin Buharin, amma ba tare da bayyana dalilin yin haka ba.

Adeshina ya ce, an maye gurbinsu da ministan muhalli Dokta Mohammed Mahmood Abubakar da kuma ministan kasa a ma’aikatar ayyuka da gidaje Abubakar Aliyu. Korar ministocin biyu na zuwa ne bayan shekaru biyu da nada su sakamakon sake zaben shugaban kasar a shekarar 2019.

Wadannan ministoci su ne na farko da shugaban ya kora tun bayan sake rantsar da shi a karagar mulki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *