Buhari ya yi watsi da Fulani -Miyetti Allah

Tura wannan Sakon

Kungiyar Fulani makiyaya ta kasa, wadda ake kira Miyetti Allah ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da laifin yin watsi da muradunsu.

Sabon shugaban kungiyar, Baba Usman Ngelzerma ya ce, yayin da Buhari ya ware makudan kudade zuwa bangarorin noma da suka hada da manoman shinkafa da nau’in abinci, babu wani shiri da gwamnatin kasar ta gabatar domin taimaka wa makiyaya.

Ngelzerma ya ce, a shekaru 8 da suka gabata, babu shirin inganta rayuwar makiyaya da gwamnati ta aiwatar da shi wadanda za su taimaka wa ‘ya’yan kungiyarsu wadanda ke ci gaba da fama da matsaloli musamman na ‘yan bindiga da barayin shanu da ke kashe ‘ya’yansu suna kwashe masu dukiyoyi.

Shugaban kungiyar ya ce, ganin tsangama da hare-haren da ake kai wa ‘ya’yan kungiyarsu, babu wadanda suka fi bukatar taimako da ya wuce su, amma kuma abin takaici har yanzu ba su ga alamar samun tallafi daga bangaren gwamnati ba.

Ya ce, ta yaya za a bar sana’ar da ta kunshi triliyoyin Nairari a hannu mutanen da ba su da ilimin zamani a kuma ce za a samu ci gaba.

Shugaban kungiyar wanda ya bayyana bangaren kiwo a matsayin wanda ke kusa da yadda man fetur ke samar wa Nijeriya kudade. “Muddin aka inganta bangaren da kuma zamanantar da shi, ba karamar arziki kasar za ta samu ba, yayin da dubban mutane kuma za su samu ayyukan yi.”

a cewar shugaban. Dangane da masu cewa, kiwo sana’a ce wadda babu hannun gwamnati a ciki, Ngelzerma ya ce, idan haka ne me ya sa gwamnati take taimaka wa kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *