Buni ya jinjina wa askarawan Nijeriya

Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya yaba wa dakarun sojan Nijeriya bisa hovvasa da bajintar da suka nuna wajen daqile harin da ‘yan qungiyar Boko Haram suka kai garin Gujba a jihar ta Yobe a ranar Asabar ta makon jiya.
A jawabin da ke xauke da sa hannun Darakta Janar kan harkokin ‘yan jaridu na gwamnan, Alhaji Mamman Mohammed ya ce, bisa ga jajircewar da dakarun tsaron ke yi wajen farauto ‘yan bindigar a duk yadda suke hakan zai sa a ci gaba da samun nasara a yaqin da suke yi da waxannan ‘yan tayar da qayar baya.
Domin qoqarin da sojojin suka yi, babban abin a yaba ne kasancewar suna yi ne domin tsaron rayukan jama’a da dukiyoyinsu.
Gwamna Mai Mala ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da bayar da goyon baya da kuma nuna yabo ga jami’an tsaron bisa ga yadda suke gudanar da ayyukansu a dukkan faxin qasar.
Ya bayar da tabbacin cewa, gwamnatinsa da al’ummar jihar Yobe za su ci gaba da goya baya ga jami’an tsaron domin ganin sun ci gaba da samun nasara a kan ayyukansu.
“Gwamnatina za ta ci gaba a bayar da tallafi da goyon baya, da duk abin da ya zama wajibi ga jami’an tsaron a qoqarin da suke yi na yaqi da Boko Haram domin ganin zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa a yankin namu”.
Mai Mala Buni ya kirayi jama’a da su ci gaba da sanar da jami’an tsaro duk wani take-taken mutanen da ba su yarda da su ba domin ganin an xauki matakin gaggawa.
Ya kuma nuna alhininsa kan faruwar hakan musamman ga al’ummomin yankin bisa harin da suka fuskanta.
Gwamnan ya kuma umarci hukumar kai xaukin gaggawa ta jihar SEMA da ta gaggauta kai xaukin gaggawa ga al’ummomin yankin da harin ya fi shafa.