Buni ya rantsar da manyan sakatarori 6

Gwamnna Buni
Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya rantsar da manyan sakatarorin dindindin guda shida a jihar. Sababbin manyan sakatarorin da aka rantsar su ne, Abba Gana Mohammed Anas da Bashir Abubakar Sadik da Adamu Tela Zimbo da Shu’aibu Ibrahim Amshi da Alhaji Bukar Kilo da kuma Isyaka Alhaji Lawan.
Bayan rantsar da sababbin sakatarorin, gwamna Buni ya taya su murna tare da cewa, su sani nadin nasu an yi shi ne bisa dacewa da cancanta, kuma kowannen su zai dace da ma’aikatar da ta dace da kwarewarsa.
Gwamna Buni, wanda yayin jawabinsa a dakin taro na Bankuet da ke gidan gwamnatin jihar, ya kara bayyana cewa, abubuwan da suka faru sun nuna wani sabon babi a gwamnatinsa.
Ya kara da cewa, gwamnati da mutanen jihar Yobe, suna sa ran tabbatar da wannan matsayi da aka nada su ta hanyar aiki tukuru, inganci da kuma kara yawan aikin da ya dace da ci gaban jihar.
A cewarsa, “Wannan gwamnatin ta bayar da fifiko sosai kan aiwatar da al’amuran gwamnati.” “Don haka, ina rokon ku da ku kasance masu bin ka’ida ku kuma kula da ayyukanku bisa ga rantsuwar mubaya’a da ofishin da kuka rantse za ku yi,” in ji shi.
Ya kuma umarce su da su yi amfani da kwarewarsu wajen bayar da cikakkiyar gudummawarsu domin inganta ayyuka ga al’ummar jihar Yobe.