Buni ya sami lambar yabo ta kasar Nijar -Saboda kyautata dangantaka

Tura wannan Sakon


Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya samu lambar yabo mai girma ta Jamhuriyar Nijar a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar.

A lokacin da yake yi wa gwamnan ado da karramawa da lambar yabo ta ‘Commandeur dans l’ordre du merite du Niger’, shugaban kasar, Mohamed Bazum na Jamhuriyar Nijar, ya ce, an karrama shi ne saboda irin gudummawar da gwamna Buni ya bayar ga alakar kasashen biyu da tattalin arziki da zamantakewa tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.

Mohamed Bazum ya ce, lambar yabon ta sanya gwamna Buni a matsayin jakadan da zai karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Da ya ke mayar da jawabi, gwamna Buni ya ce, ya samun kwarin gwiwa dangane da lambar yabon hade da karramawar kasa da ya samu daga shugaban kasar Jumhuriyar Nijar.

“Karramawar ta kasa da aka ba ni, za ta zaburar da ni in kara yin aiki a kan muradun kasashen biyu.”

“Jihar Yobe tana da iyakokin kasa da kasa da Jamhuriyar Nijar, saboda haka, za mu karfafa zaman lafiya da wadatar tattalin arziki tsakanin al’ummomin kan iyakokin kasashen namu biyu,” in ji shi.

Gwamnan ya samu rakiyar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan da ‘yan majalisar dokoki ta kasa da na jiha, da majalisar zartarwa ta jiha, da ‘yan siyasa, da dubban masu fatan alheri a fadin kasar baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *