Buni ya taya Tinubu murna

Tura wannan Sakon

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya taya zababben shugaban Nijeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima murnar nasarar da suka samu a rumfunan zaben da ya gudana.

Hakan yana kunshe a cikin wata sanarwa da Alhaji Mamman Mohammed Daraktan yada labarai da harkokin ‘yan jaridu na gwamna ya sanya wa hannu kuma aka mika wa manema labarai a Damaturu.

Buni ya bayyana Tinubu da Kashim a matsayin mafikyawun tawagar Nijeriya a wannan lokacin da ake ciki. Al’ummar Nijeriya sun yi magana da kyakykyawan fata na ganin Nijeriya ta gyaru ta hanyar shugabancin Tinubu/ Shettima. Tinubu dan Nijeriya ne na gaske wanda a rayuwarsa ta sirri da ta sarari yana daukar ‘yan Nijeriya daga kabila, al’adu da addinai daban-daban.

“Kwarewarsa na sauya jihar Legas ko shakka babu zai yi amfani da shi wajen kawo sauyi ga wannan babbar kasa ta mu Nijeriya.”

Gwamnan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da suka hada da sauran ‘yan takara da suka fafata tare da shi da su marawa zababben shugaban baya domin gina kasa mai dunkulewar kasa baki daya.

Gwamna Buni ya yi addu’ar Allah ya yi wa gwamnatin Asiwaju/Kashim jagora domin samun hadin kai, wadata da kuma ingantuwar Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *