Bunkasa ilimi: Shehu Bala Usman ya cancanci yabo – Jama’ar gari

Alhaji Shehu
Daga Mohammed Ahmed Baba Jos
Alhaji Shehu Bala Usman shi ne shugaban karamar hukumar Jos ta arewa, ana yaba masa da irin namijin kokarin da yake yi tun kafin ya hau kujerar Shehu Bala ya rike matsayin sakataran karamar hukumar Jos ta arewa, tun daga wannan lokacin.
Ya yi wa al’umma ayyukan ci gaba inda tun daga a wannan lokaci a shekarar 2016 ya samarwa mutane 13 gurbin karatu a jami ar Jos, kuma yake biya masu kudin makaranta a shekarar 2017 ya samarwa mutane 4 gurbin karatu Suma a jami ar ta jos, sannan akwai.
Mutane 70 da ya samar musu koyarwa a makarantar firamare sannan akwai mutanen da suka sami aikin ( cibic Defence) su 13 a shekarar 2016 mutane 4 sun sami aikin (Air force) da kuma mutane 5 da ya samarwa aiki a ma aikatar karamar hukuma, a fannin sana oin hannu an koyawa.
Marayu 35 sana’o’i da kuma tallafa masu a bangarori da dama, domin samun saukin rayuwa yawancin wadannan ayyukan ya yi su ne lokacin yana matsayin sakataran karamar hukuma, wannan ayyuka da ya yi ne yasa mutane da dama suke kira cewa, ya fito.
Takarar shugaban karamar hukumar Jos ta arewa, kuma bayan ya fito yayi nasara a zaben fitar da gwani a jam’iyyar Apc, sannan gwamna Simon Lalong ya tabbatar mai da kujerar ta shugaban karamar hukumar, inda nan gaba za a gudanar da zabe a watan oktoba.
Mai zuwa na kananan hukumomi inda a baya ba a gudanar da zabe a kananan hukumomi guda hudu ba, kamar Jos ta arewa Jos ta kudu, basa da Riyom saboda matsalar tsaro, amma a wannan karon gwamnati ta tabbatar da cewa za a yi zaben gaba daya a kananan kumomin.
A fadin jihar Filato a watan 10 mai zuwa bayan ya zama shugaban karamar hukumar ya bayar da (transformer)a unguwannin mudi na garba, haruna hadeja, da kuma unguwar idi mai borkono, sai unguwar rimi inda matasa kimanin 15 da suka sami aikin soja.
Da kuma mutanen da shugaban ya bai wa tallafin karatu a jami’ar Jos mataimaki na musamman akan ayyukan yau da kullum, ga shugaban Muhammad shala ya bayyanna cewa, an yi aikin ruwa inda aka saka fanfunan ruwa da makarantun firamare da suka sami tallafi.
Kamar makarantar islamiyya dake bauchi road wacce itace mafi dadewa a garin Jos da makarantar U.N.E. da ke Nasarawa, da sauransu ya ce” suna aiki Musulmai da Kirista tare a karkashin shugaban domin kara hadin kai da zaman lafiya a garin Jos, da unguwanni.
Shugaban ya tabbatar da tsaftar muhalli, na wata wata wanda a baya dokar ta yi sanyi an tabbatar da hana cinkoso a babbar kasuwar terminus da titin Ahmadu Bello inda a baya abin yake ci wa mutane tuwo a kwarya, amma yanzu jama’a suna yaba wa saboda doka.