Burina, ci gaban al’ummar D/Kudu, Warawa -In ji Mustapha

Mustapha Bala Dawaki

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa a majalisar tarayya, Alhaji Mustapha Bala Dawaki, ya bayyana cewa, babban burinsa shi ne ci gaban alummar Dawakin Kudu da Warawa musamman wajen samar masu da ayyukan-yi ga matasa maza da mata.

 Ya ce, duk wani dan siyasa a duniya, burinsa shi ne ya ga cewa al’ummarsa suna tare da shi, kuma a mulki irin na dimokaradiyya, kwalliyar dan siyasa ita ce jama’a.

Dawaki ya yi wannan furuci a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a wajen bikin daurin aure, wanda ya gudana a garin Matage, a karamar hukumar Dawakin Kudu, a makon da ya wuce.

Ya kara da cewa, banbancin da ke tsakaninsa da sauran ‘yan majalisa shi ne, a koda yaushe yana tare da jama’a, kuma a cikin duk mako yana ware kwana hudu a mazabarsa tare da jama’a domin jin koke-kokensu da matsalolinsu, kuma kwana ukun da suka rage a mako yana majalisa, domin gabatar da koke-koke da matsalolin al’ummar a majalisa.

 Mustapha ya yi kira ga sauran ‘yan majalisa da su yi koyi domin ta hakan ne kawai za ka san matsalolin da ke damun jama’a musamman mazabar da kake wakilta.

Dan majalisar ya bayyana shekaru 23 da komawa mulkin dimokuradiyya a Nijeriya da cewa an sami nasara da kuma ci gaba daban-daban.

Ya ce, a cikin wannan shekaru 23 da komawa mulkin dimokuradiyya, Nijeriya ta shiga sahun kasashen duniya wajen bayar da ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma samar da gwamnati ta al’umma wadda jama’a suka zaba, don haka yana nuna irin ci gaba da aka samu a kasar nan da kuma jihohi.

Daga karshe, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da bai wa gwamnatin APC goyon baya domin gudanar da ayyukan alheri ga al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *