Burina, wakilci nagari ga al’ummata -Ummul-khairi

Barista Amina Ummul-Khairi Ibrahim BB Faruk

Barista Amina Ummul-Khairi Ibrahim BB Faruk

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

Mai neman takarar kujerar majalisar tarayya a kananan hukumomin Gezawa da Gabasawa a karkashin jam’iyyar PDP, Barista Ummul-Khairi Ibrahim BB Faruk ta bayyana dalilanta na fitowa takarar majalisar tarayya da cewa, samar da ingantaccen wakilci nagari ga al’ummar Gezawa da Gabasawa shi ne babban burin ta.

Ta ce, shekaru 23 da mulkin dimukuradiyya a Nijeriya al’ummar kananan hukumomin Gezawa da Gabasawa har yanzu ba su gani a kasa ba, saboda rashin wakilci nagari.

Ummul-khairi ta bayyana haka ne a lokacin da take tattaunawa da manema labarai ciki har da wakilin jaridar Albishir a ofishinta da ke birnin Kano satin da ya gabata.

ci gaba Ta ce, kamar yadda aka sani cewa, dimukuradiyya mulki ne da ke bai wa al’umma fadin albarkacin baki da cikakken ‘yanci da kuma uwa uba kafa gwamnati ta al’umma wanda jama’a suka zaba domin haka a matsayin ta na mai neman kujerar majalisar tarayya zata kawo sauyi da canji wanda jama’a za su gamsu da cewa, yanzu aka samu wakilci nagari idan har ta samu nasarar zabe.

Ta kara da cewa, a ko’ina a duniya aikin dan majalisa shi ne samar da doka da oda da kuma samar da kudurori wanda za su kawo ci gaban jama’a da kare lafiyarsu da dukiyoyinsu, saboda haka nasarori ba sa samuwa sai da hadin kan jama’a kuma za mu kafa kwamiti wanda aikinsa sauraron koke-koken jama’a da hanyoyin da za’a bi domin samun nasara.

Barista ta ci gaba da cewa, a cikin kwamitin dole sai dan asalin Gezawa ko Gabasawa kuma mazaunin gari wanda kuma yake tare da al’umma kullum kuma ba za a saka bako ba a cikin kwamiti kuma za mu kafa kwamiti a kowace mazaba domin ta haka ne za ka fahimci ta ina za ka fara kuma ta ina za a samu nasara.

Ummul-khairi ta ce, idan har ta ci zabe za ta bunkasa harkokin noma musamman dam din Wasai domin samar da aikin yi ga manoman rani da damina wanda akalla manoma dubu 20 za su amfana kuma wajen harkar ilimi akwai tanadi da taste-tsare na musamman domin bunkasa harkar ilimi a mazabar da kuma tabbatar da an kawo wani bangare daga jami’ar Bayero da ke Kano domin saukakawa matasa da kuma ci gaban al’umma da ke kananan hukumomin Gezawa da Gabasawa wajen harkar ilimi.

Ta kara da cewa, ganin yadda harkar lafiya take a yanzu na rashin kwararrun likitoci da kayan aiki wadatat tu a asibitoci wanda hakan ya haifar da matsaloli dabamdabam na harkar lafiya a kananan hukumomin Gezawa da Gabasawa domin haka za mu samar da yanayi mai kyau na kyautatawa harkar lafiya da makamantansu a mazabar.

Ta kara da cewa, za mu gyara hanyoyi da tituna domin saukakawa al’umma wajen fito da amfanin gonar su da kuma tafiye-tafiye na yau da kullum.

Daga karshe, ta yi kira ga al’ummar Nijeriya da su fito kwansu da kwarkwatar su da su zabi jam’iyar PDP daga kasa har sama domin zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban al’umma da kuma bunkasar tattalin arzikin kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *