Burinmu, matasa a sahun gaba wajen kwallon kwafa – Gwamnatin Kano

Jihar Kano
Tura wannan Sakon

Daga Rabiu Sanusi Kano

Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta tabbatar da kudurinta na ganin matasan jihar sun taka rawar gani a idon duniya a harkokin wasanni.

Bayanin hakan ya fito daga bakin kwamishinan wasanni da walwalar matasa na jihar Kano, Kwamared Kabir Ado Lakwaya, sa’ilin da yake mika tallafin kayakin wasan kwallon kafa ga wasu kulob-kulob sama da 200 a yayin ziyararsa a kananan hukumomi bakwai.

Kananan hukumomin da suka rabauta sun hadar da Tudun Wada da Doguwa da Rano da Kibiya da Bunkure da Warawa da kuma karamar h ukumar Dawakin Kudu,Wanda daga kowace karamar hukuma a ka zabo kungiyoyin wasanni 20 daga ko’ina daga matakin karamar kungiya.

Lakwaya ya ce, kamar yadda gwamnan jihar Kano ya dakko su a matsayin masu ba shi taimaka masa ta fuskar wassani da walwalar jama’a, don haka suka ba shi shawarwari kan yadda za a taimaka wa matasa wajen bunkasa kwallon kafa.

Kwamishinan ya ce, shirya-shirye sun yi nisa wajen sama wa ‘yan wasan jihar Kano da aka fi sani da Kano Pillars gurin wasa na bai-daya tare da samar masu alawus da albashi mai kyau da kara bunkasa harkokin wasanni a jihar.

“Baya ga wasa kwallon kafa, akwai sauran wasanni daban-daban da gwamna ya bayar da damar a farfado da su domin a bai wa matasa maza da mata damar shiga a dama da su.”

A jawaban da suka gabatar yayin karbar kayan daga shugabannin kananan hukumomin da kuma wasu daga cikin wakilansu, irin su, Honarabul Matate, daga karamar hukumar Tudun Wada da Honarabul Umar Gado-Gado, daga karamar hukumar Warawa, sun nuna matukar godiya bisa kulawa da matasa.

Sun kuma bayyana cewa, yadda akai masu wannan kabakin alkahiri, su ma a shirye suke wajen ganin sun mayar da biki a ranar zabe cikin yardar Allah, nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, bisa haka, za su yi zabe bisa cancanta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *