Saboda hauhawar farashin kayan masarufi -Gidajen abinci sun yi karin farashi -In ji Abubakar
Daga Musa Diso Manajan gidan abincin Shab`an da ke kan titin gidan Zoo, Malam Yahaya Abubakar ya bayyana hauhawar kayan masarufi musamman kayan abinci da cewa, wani babban kalubale ga ‘yan Nijeriya da ke fuskanta a wannan lokaci na rashin tabbas. Manajan ya yi furucin ne ga wakilin jaridar Albishir a babban birnin Kano makon […]
Samar da fetur: IPMAN ta yi barazanar kawo cikas, muddin…
Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN ta bayyana dalilan da suka haddasa cunkuson ababen hawa a gidajen mai, musamman a Abuja babban birnin tarayya da kuma wadansu jihohi, saboda abin da ta kira na dakatar da dakon mai, a sassan kasar. Yanzu haka kungiyar ta IPMAN ta yi barazanar dakatar da sayar da man […]
A Yobe: NDE ta horar da matasa 100 kan dabarun kasuwanci
Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu Hukumar kula da ayyukan yi ta kasa (NDE) reshen jihar Yobe tare da hadin gwiwar Nazeemursaj Nigeria Limited sun fara horar da matasa da mata 100 marasa aikin yi na kwanaki biyar a kan dabarun kasuwanci. Darakta Janar na hukumar ta NDE, Abubakar Nuhu Fikpo, a lokacin da yake bayyana […]
A tabkin Chadi: Zulum ya gwangwaje masunta da Motoci 5
Sani Gazas Chinade, Daga Maiduguri Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da tallafin motoci 5 da kudade ga wadansu masunta da ‘yan-kasuwa da ke yankin Tabkin Chadi. Da yake gabatar da jawabi, gwamnan ya ce, tallafin da ake bai wa masunta da ‘yan kasuwar kifi, an yi haka ne domin a karfafa […]
A Kano: Farashin kayayyakin abinci ya sauka -In ji Dan Ibadan
Labari daga Musa Diso Kakakin kungiyar masu sayar da hatsi da ke kasuwar Dawanau, Abubakar Ibrahim Dan Ibadan ya ce, saboda mahimmancin wannan wata na Ramadan kungiyar kasuwar Dawanau ta samar da rangwamen farashin kayan abinci domin samun falalar watan. Ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilin Albishir a birnin […]
A Ikko: Hukumar hana fasa-kwabri ta kama jirage da kayan sojoji
Hukumar hana fasa-kwabri, shiyar jihar Ikko, ta ce, ta kama jirage marasa matuka da kayan sojoji da wadansu miyagu suka yi fasa kwabrin su. Hukumar da ke kula da filin jiragen sama na kasa da kasa da ke birnin Ikko ta bayyana haka ne ranar Talatar da ta gabata kuma ta kiyasta cewa, kudaden kayayyakin […]
Rike sana’a da gaskiya kan taimaka wa dankasuwa -Ibrahim Tarauni
Daga Rabiu Sunusi An hori Yankasuwa dasu zama masu kamanta gaskiya da tsoron Allah yayin gabatar da harkokin kasuwancinsu koda yaushe. Shugaban kungiyar masu gyaran kaji da sai kajin na kasuwar karamar hukumar Tarauni awata zantawa da ALBISHIR. Tarauni yace lallai kodayaushe idan Mai sayen kayanka yazo yaga kakamanta mashi yayin gudanar da wannan kasuwanci […]
A Ikko: Shugaba Buhari ya bude kamfanin taki – Mallakin Dangote
Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci qaddamar da kamfanin samar da takin zamani da ke cikin katafariyar matatar man fetur mallakin Aliko Dangote a jihar Ikko. Matatar da ke matsayin irinta ta farko kuma mafi girma a nahiyar Afrika, wadda aka kashe tsabar kudi dala biliyan 2 da rabi, da kuma ake sa ran ta samar […]
A Kano: Masu sayar da manja, mangyada sun rage farashi’
Daga Ahmad S. Ahmad Shugabancin kungiyar masu sayar da manja da mangyada na kasa reshen kasuwar Galadima karkashin jagorancin Alhaji Muhammad Wada Yahaya sun tabbatar da samun raguwar farashin manja da mangyada, wanda a baya farashin ya kai Naira dubu 23, wanda a yanzu farashin yanzu ba ya haura 19 zuwa dubu 20. Alhaji Muhahammad […]
A Kano: Fiye da mutane dubu 36 ke sana’ar tifa -Kwamred Mamuni Takai
Fiye mutane dubu 36 suke cin abin a bangaren sana’a ta aikin tifa a fadin jihar Kano. Hakan na fitowa ne daga bakin shugaban hadaddiyar kungiyar direbobin tifa na kasa reshen jihar Kano, Kwamred Mamu Ibrahim Takai a wata zantawa da wakilin Albishir makon jiya. Kwamred Mamu ya kuma tabbatar da cewa, lallai tafiyar ta […]