A Kano: Salka Media ta rarraba wa marayu 650 tufafin sallah
Daga Ahmad S Ahmad A karshen makon da ya gabata ne wadansu marayu suka rabauta da kayan sallah wanda Gidauniyar Salka Media ta ba su domin su ma a dama da su a yayin bukuwan salla karama mai zuwa. Shugaban Gidauniyarkuma dan jarida, Sani Ahmad Sagagi ya bayyana wa manema labarai cewa, sun bayar da […]
An gano dabarun noman dawa -Abdullahi Ali
Shugaban qungiyar masu noman dawa a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Ali Maibiredi, wanda kuma shi n e shugaban hadaddiyar qungiyar manoma ta qasa reshen jihar Kano (AFAN) ya bayyana cewa, a yanzu manoma sun sake farkawa kan noman dawa domin amfanin al’umma, kasancewar an gano ana yin abubuwa da yawa da ita, wadanda suka hadar […]
A Ikko: Shugaba Buhari ya bude kamfanin taki – Mallakin Dangote
Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci qaddamar da kamfanin samar da takin zamani da ke cikin katafariyar matatar man fetur mallakin Aliko Dangote a jihar Ikko. Matatar da ke matsayin irinta ta farko kuma mafi girma a nahiyar Afrika, wadda aka kashe tsabar kudi dala biliyan 2 da rabi, da kuma ake sa ran ta samar […]
Zaman Lafiya, ci gaban al’umma –Aremu
Daga Rabiu Sunusi A ranar Talata ne kungiyar wanzar da zaman lafiya da kawo sasanci da sulhu tsakanin mutane ta jihar Kano da hadin gwiwa da kungiyar gamayyar Turai bisa jagorancin majalisar kasar Birtaniya sun gudanar da taron bita ga membobinsu bisa yadda za su shiga lungu da sako don wayar wa da al’umma kai […]
Kashe-kashen shanu: Abia za ta biya Fulani diyya
Gwamnatin jihar Abiya ta fara biyan diyya ga mutanen da hari da aka kai a sabuwar kasuwar shanu ya shafa. Bayanin na zuwa ne bayan da gwamna Dokta Okezie Bictor Ikpeazu na jihar ya gana da al’ummar Hausa-Fulani mazauna jihar kan harin. Sarkin Hausawan Aba, Shehu Bello ya shaida wa wakilinmu cewa, gwamnan ya fara […]
Za mu kwato wa kanawa hakkinsu bangaren noman dawa -Badamasi Bunkure
Labari Rabiu Sunusi daga Katsina Kungiyar manoman dawa ta kasa reshen jihar Kano ta bayyana sabon shirinta na mayar da martabar noman dawa a jihar Kano. Hakan ya fitodaga bakin shugaban kungiyar na jihar, Malam Badamasi Bunkure a wata zantawa da Albishir makon da ya gabata. Bunkure ya bayyana cewa, lallai su ya zuwa yanzu […]
Gwamnati, a taimaka wa manoma na gaskiya -In ji Mado
Matukar gwamnatin kasar nan tana son ciyar da kasar nan da abinci, to babu shakka sai ta mayar da hankalin ta wajen taimaka wa tsantsan manoma na gaskiya, saboda yawancin taimakon da take bayar wa ba ya zuwa ga manoman da ake bukata. Baynin haka ya fito ne daga bakin wani manomi dankasuwa da ke […]
Matasa, a kama sana’ar noma -In ji Ali Branco
Daga Jabiru Hassan An yi kira ga matasan jihr Kano da su kama sana’ar noman rani da damina domin ci gaba da kasancewa cikin zamantakewa mai albarka da kuma amsa kiran gwamnatin tarayya na wadata kasa da abinci. Kiran ya fito ne daga Ali Adamu Kunnawa wanda aka fi sani da Ali Branco da ke […]
Borno ta amince da kaddamar da shirin ruga
Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu Gwamnatin jihar Borno ta amince da kaddamar da shirin nan na gwamnatin tarayya, domin makiyaya Ruga da zimmar zaunar da makiyayan da rikicin Boko Haram ya shafa da suka rasa wuraren kiwo. Shiri na gwamnatin Borno domin makiyaya a cewar gwamnatin za a samar da shi ne a yankuna uku […]
A Bauchi manoman rani za su kwashi garabasa -In ji Bappa Misau
Daga Sule Aliyu , Bauchi Alhaji Bappah Aliyu Misau sarkin yamman Misau kuma shi ne shugaban kamfanin samar da takin zamani na jihar Bauchi, ya zanta da manema labarai kan yadda suke kokarin samar da takin ga manoma masu yin noman rani a jihar da kuma jihohin makwabta bayan sun samar da takin noman damina […]