Chanchanta ta sa muke marawa Inuwa Ibrahim Waya Baya – Babangida Aliyu Sharada

Inuwa Ibrahim Waya Baya

Inuwa Ibrahim Waya Baya

Tura wannan Sakon

Daga Rabiu Sanusi  Kano

Anbayyana cancanta amatsayin dalilin da yasa Malam INUWA WAYA yakamata Yazama gwamnan jahar kano a zaben da zai zo nan da shekara Mai zuwa idan Allah yakaimu.

Hakan na fitowa ne daga bakin dankishin samar da cigaba ga Al’ummar jihar Kano watau Malam BABANGIDA ALIYU SHARADA a wata zantawa da jaridar ALBISHIR ranar laraba.

SHARADA,ya kara da cewa malam Inuwa waya na sahun manyan mutanen da ke bukatar ganin jama’ar Kano sun kara nausawa cikin cigaba ta kowace fuska.

Sannan Babangida sharada ya Kuma cewa wannan bawan Allah kasancewar shi ma’aikaci a gwamnati bai hana shi ra’ayin tsayawa takara dan magance matsalolin da ya ke hange na tunkaro al’ummar jihar Kano ba.

Haka nan ma yace duk kasancewar shi lokacin aje aikin sa baiyi ba amma ya amince ya aje yazo dan hidimtama jama’ar shi ba wajen kawo ma su cigaba da sauran su.

Haka zalika kasancewar inuwa Ibrahim waya mamallakin Gidaunyar RABA GARDAMA da ke tallafama al’umma ta fuskar da ta dace kama daga kayan makaranta, litattafai uniform da dai sauran su na daya daga cikin abin ke kara mashi karfi wajen taimakon al’umma.

Kazalika ya kara dacewa Inuwa waya ya kware wajen taimakon al’umma wajen samar ma jama’a gudunmuwar yin rajista ta ga daliban da suka samu gurbin karatu ga kama daga jami’a da sauran manyan makarantun su ka samu.

Sannan Babangida ya tabbatar da cewa lokacin da gwamnati jihar kano ta bullo da batun ilimi kyauta ga mutanen Kano lallai Inuwa waya ya yi matukar farin ciki dan kuwa bai da burun da ya wuce yaga matasa na karatu da neman ilimi, hakan ma yabashi damar kara kaimi wajen taimakon da yake ma ma su bukatar samun gurbin karatu na gaba da sakandire da ma matakin kasa da haka.

Haka Kuma ya magantu kan batun lalacewar matasan mu wajen harkar shaye shaye da daba da shan shisha da yakara kamari, dan haka yace lallai yana da kudurin kawo gyara a wannan fannin.

Ya kuma kara da cewa kasancewar shi mai kyakkyawan niyya yasa su ka amince da tafiyar shi ta hanyar da suma yakamata su bada ta su gudunmuwar wajen magance matsalolin da su ke bijiro ma jahar kano.

SHARADA wanda ya kwashe tsawon lokaci wajen tafiyar Yan siyasa daban daban tun lokacin da mai girma shugaban kasa Muhammadu buhari har izuwa Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje da yazama zakaran gwajin dafi a sauran gwamnoni wajen ayuka da yawa.

Haka Kuma ya ce ganin yadda Malam INUWA IBRAHIM WAYA yake taimakon al’umma ne mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ba shi shawara da yafito takarar gwamnan jahar kano dan cigaba da tabbatar kudurin sa ga Al’umma.

Babangida wanda yakara jawo hankalin iyaye kan batun sa ido ga tarbiyyar yaran su koda yaushe, dan kuwa ubangiji ne yaba su kiwon yaran su Kuma su sani cewa zai tambaye su abinda ya ba su kiwo, Dan haka ya kara jan hankalin kan kowa nada hakkin bada tarbiyya ba sai Mutum daya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *