Ci gaba da yajin aikin ASUU, zaizayewar karatu -Kwamared Jingau

Yajin aiki: ASUU ta bayar da wa’adin makonni 3

Tura wannan Sakon

Daga wakilinmu

Akwai hadari da kuma damuwa sosai matukar kungiyar malaman jami’oi ASUU ta ci gaba da yajin aikin da suke yi yanzu haka, saboda haka ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta gaggauta biyawa malaman hakkokinsu cikin hanzari ko daliban za su samu damar komawa makarantunsu.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin Kwamared Aminu Abdullahi Jingau, a lokacin da yake zantawa da manema labarai. Wadanda za su tsaya wajen kawo karshen yajin aikin malaman yawancin yaransu ba’a kasar nan suke karatu ba, idan ma nan suke karatu za ka samu suna jami’a ce ta kudi, wannan ya sa muke tare da kungiyar ta ASUU kuma za mu ci gaba da mara mata baya har sai ta kai ga samun nasara da yardar Allah.

Kwamared Aminu Abdullahi Jingau, ya ce, lalacewar tsaro a kasarnan idan ka bincika a kwai hannun wadannan dalibai sakamakon rashin bude jami’oin kasar nan. Jingau wanda har ila au shi ne mai unguwar rukunin gidaje na Ibrahim Kunya da ke unguwar, Farawa ya ce, za su ci gaba da bin matakan da suka dace wajen kawo karshen yajin aikin.

Daga karshe, ya nuna matukar farin cikinsa game da yadda wadansu gwamnonin suka nuna damuwarsu a kan danbarwa tsakanin gwamnati da kugiyar ASUU.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *