Cigiya: Ko Ka Ga Babangida?

Muna Cigiyar Babangida

Tura wannan Sakon

A ranar 9 ga Fabrairu 2022 muka sami labari daga iyalan Alhassan Ahmad (Babangida) kan bacewarsa.

Mai kimanin shekaru 45 da haihuwa, Alhassan wanda aka fi sani da Babangida yana zaune a unguwar Gwammaja Layin ‘Yancharkwai a karamar hukumar Dala da ke cikin birnin Kano.

Yau fiye da makonni biyu kenan ba a ji duriyarsa ba ko ta waya ko ta wani mutum wanda ya san shi. Har ila yau, babu wani kira daga masu satar mutane domin neman fansa.

A saboda haka muke fatan duk wanda ya gan shi ya sanar da ofishin ‘yansada mafi kusa ko ta lambar waya 08061545405 ko 07031001715

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *