Cikar Nijeriya 62: Al’umma a zabi shugabanni nagari

Talban Panshekara, Alhaji Isyaku Yahaya

Talban Panshekara, Alhaji Isyaku Yahaya

Tura wannan Sakon

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An yi kira ga al’umma su ci gaba da bayar da goyon baya dan samun ci gaba da dorewar kasar nan dunkulalliya mai amfani ga al’ummarta.

Talban Pansheka, Alhaji Isyaku Yahaya ne ya bayyana hakan da yake bayani a kan nuna farin cikinsa ga cikar kasar nan shekaru 62 da samun ‘yanci.

Ya ce, duk wata kasa da ta samu ci gaba za a ga al’ummar ta suna zaune lafiya duk kasar da ba hadin kai da zaman lafiya za ta tabarbare domin haka yana addu’a Allah ya kawowa Nijeriya zaman lafiya da ci gaba.

Talban Panshekara ya yi kira ga ‘yan siyasa su yi yakin neman zabe mai zuwa cikin natsuwa da zaman lafiya da fatan samun shugaba nagari da zai dorar da ci gaba da zaman lafiya da tsaro. Ya yi kira ga ‘yan siyasa da suke takara su sanizabe abu ne na Allah duk wanda Allah ya zaba shi zai nasara.

Alhaji Isyaku Yakasai Talban Panshekara ya yi kira ga al’umma su zabi ‘yan takara masu inganci a kowane mataki wanda zai nuna kishin al’umma da zai kawo ci gaba. Wannan kasa na son shugaba nagari, ingantacce da al’umma za su kawo ci gaba a kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *