Cikin sakonnin Sallah: Sarakunan Kano sun yi horo da a yi wa kasa addu’a

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Masu Martaba sarakunan Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da na Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero da Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar da na Rano Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa da kuma Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya sun bukaci al’ummar kasar nan da su kara yi wa Nijeriya addu’oi na samun dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowane lokaci.

Sun yi horon a sakonninsu na barka da Sallah jim kadan bayan kammala Sallar idi da aka gudanar a masarautunsu, inda suka jaddada cewa, yawaita addu’oi zai kawo karshen dukkanin wadansu abubuwa da ke wakana na tashe-tashen hankula da kuma rashin tsaro.

Haka kuma sarakunan sun yi kira ga al’umominsu da su ci gaba da yin aiki da abubuwan da suka koya lokacin azumi wanda hakan zai kyautata zamantakewa da mu’amulla kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, inda kuma suka yi fatan alheri ga Musulmin duniya bisa zagayowar karamar Sallah.

Haka kuma sarakunan sun gudanar da bukukuwan hawa da zagaya wa muhimman gurare inda suka gaisa da al’umominsu a dukkanin masarutun Kano da Bichi da Gaya da Karaye da kuma Rano kamar yadda aka saba, yayin da rahotanni suka tabbatar da cewa, an yi shagulgulan karamar Sallah cikin farin ciki da raya al’adun Hausa.

A karshe, sarakunan guda 5 sun yaba wa gwamnatin jihar Kano bisa jagorancin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda kokarin da take yi wajen inganta tsaro da gudanar da ayyukan alheri a fadin jihar kamar yadda ake gani a kowane lungu da sako ba tare da nuna kasala ba. Bugu da kari, dukkanin mutanen da wakilinmu ya yi magana da su sun bayyana jin dadinsu na yadda aka gudanar da bukukuwan karamar Sallar bana cikin nasara tare da fatan cewa, a babbar Sallah idan Allah ya kai mu za’a sami kyakyawan yanayi na gudanar da shagulgulan Sallah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top