Cikin shekaru biyu: Manoman Birnin Gwari sun biya ‘yan-bindiga Naira miliyon 400

Manoman Birnin Gwari sun biya ‘yan-bindiga Naira miliyon 400
A Birnin Gwari da ke jihar Kaduna sun ce akalla Naira miliyan 400 manoma suka biya ‘yan bindiga cikin shekaru biyu, domin ba su damar yin aiki a cikin gonakinsu, amma duk da haka ba su tsira ba.
Daya daga cikin shugabannin al’ummar yankin, Alhaji Zubairu Abdura’uf ya shaidawa cewa, idan har mahukunta ba su bar al’umma sun kare kansu ba, to lalle kuwa za’a iya fuskantar matsalar karancin abinci a wannan shekara.
AbduRra’uf ya kara da cewa, a shekarun baya manoman yankin Birnin Gwari na samar da abincin da yawansa ya kai akalla tan 700 na hatsi, amma a yanzu tuni labara ya sha bamban la’akari da cewa, mutanen ba sa iya zuwa gonakinsu.
Birnin Gwari na daga cikin yankunan da suka fi fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a jihar Kaduna mai fama da matsalar tsaro a sassanta, inda ‘yan ta’addan suka addabi mazauna yankin ta hanyar kashe rayuka da satar mutane domin karbar kudin fansa.