Cin zarafi: Kuliya manta sabo ya daure Sadiya Haruna

Daga Zainab Sani Shehu Kiru Wata Kotun Majistire da ke filin jirgin saman kasa da kasa na Malam Aminu Kano, ta yanke wa jarumar Kannywood kuma fitacciyar mai amfani da shafin Instagram dn nan, Sadiya Haruna, hukuncin zaman gidan gyaran hali na wata shida sakamakon cin zarafin wani jarumin Kannywood, Isah Isah.
Rahotanni sun ce, Sadiya Haruna ta ci zarafin Isah Isah ne a Instagram inda ta yi amfani da kalamai masu kaushi, abin da ya harzika Isah Isah shi ya maka ta a kotu. Sadiya Haruna ta bayyana a cikin wani gajeren bidiyo cewa, Isa ya yi auren mutu’a da ita kuma ya sadu da ita ta dubura ba tare da son ta ba.
Ta kuma kira shi mai neman mata, mai neman maza da dai sauran munanan kalamai da Labarai24 ba za ta iya wallafawa ba.
An maka ta a kotun ne ranar 16 ga Okutoba, 2019 bisa zargin bata suna, abin da ya saba wa Sashi na 391 na Penal Code. Da yake yanke hukuncin ranar Litinin din nan, mai Shari’a Muntari Dandago, ya yanke wa Sadiya Haruna hukuncin zaman gidan yari na wata shida ba tare da zabin tara ba.