Cin Zarafin Mata: Lauyoyi mata za su ci gaba da yaqi -Barista Amina Umar

Daga Jabiru Hassan
Kungiyar lauyoyi mata wadda akafi sani da “ International Federation For Women Lawyers” (FIDA) Zara ci gaba da yin aiki wajen kare martabar mata da fara kanana wajen yin yaki da yin zarafin da sukan fuskanta cikin al’uma, tareda tabbatar da ganin cewa ana yin hukunci mai tsanani ga dukkanin wadanda ake samu da laifi na cin zarafin mata.
Wannan bayani ya fito ne daga sakatariyar kungiyar ta FIDA a jihar Kano, Barista Amina Umar a hirar su da wakilin mu a ofishin kungiyar, inda ta sanar da cewa an kafa wannan kungiya ce domin yin aiki wajen kare martabar mata da yara kanana musamman idan an ci masu zarafi ko tauye masu wasu hakkoki nasu bisa son zuciya.
Tace kungiyar lauyoyi mata tana bakin kokarin ta wajen tabbatar da cewa ana yin hukunci kan duk wani korafi kan cin zarafin mata da kananan yara da yaje hannun su, sannan kungiya tana yi ne kyauta batare da ana biyan komai ba, wanda hakan ya taimaka wajen kyautata zamantakewa da kuma bin dokoki a tsakanin al’uma.
Batista Amina Umar ta kuma bayyana cewa kungiyar lauyoyi mata a jihar kano tana aikin wayar da kan al’uma dangane da aiyukan da suke gudanar wa domin kare martabar mata da kananan yara, sannan tace suna yin aiki na hadin gwuiwa tsakanin ta da ofishin jakadancin kasar Jamus da kungiyar Isa Wali wajen shiga lunguna da sako-sako na yankunan karkara domin fadakar da al’uma kan cin zarafin mata da kananan yara domin wayar da kai kan gabatar da korafi ga kungiyar ta FIDA.
Batista Amina Umar tace kungiyar tasu tana samun kudaden gudanar da aiyukan ta ne daga karo-karo da yayan kungiya keyi a junan su, sannan suna samun dan wani tallafi daga wasu kungiyoyin duk da cewa akwai bukatar samun taimako daga sauran bangarori ta yadda aiyukan su zai ci gaba da tafiya cikin nasara.
Haka kuma tace akwai kyakykyawar dangantaka tsakanin kungiyar su ta FIDA da hukumomin tsaro kamar yan sanda da alkalai da kafafen yadda labarai da ma’aikatar mata ta jihar kano da hukumar gyaran halida kuma shugabannin al’uma, inda a karshe tayi godiya ga gwamnan jihar kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda yunkurin da yake yi na baiwa kungiyar tasu gudummawar motar gudanar da aiyukan ta da kuma samun ofishin kungiyar na dindindin.