Cinikayya:Barca ta ci ribar fam miliyan 86

barcelona

barcelona

Tura wannan Sakon

Barcelona ta sanar da cin ribar kasuwancin £86m a shekarar da ta gabata, tana sa ran samun ribar £240m a shekara mai zuwa in ji kungiyar.

A bara kungiyar ta kasa daukar sabbin ‘yan kwallo, saboda bin dokar kashe kudi daidai samu ta hukumar La Liga.

Barcelona ta fada matsin tattalin arziki a bara, wadda ta yi hasarar £422m da ta kai Lionel Messi ya bar Camp Nou zuwa Paris St Germain..

Duk da hakan kungiyar ta kare a mataki na biyu a La Liga, amma ba ta taka rawar gani ba a sauran wasannnin da ta fafata a kakar da ta wuce.

Daga baya ne kungiyar ta dauki matakan da suka dace don mayar da kungiyar cikin jerin fitattu a fannin taka leda a duniya. Barcelona ta ce ta samu kudin shiga da ya kai £890m a kakarr 2021/22.

Kungiyar ta ci karo da tsaiko kafin ta yi wa sabbin ‘yan kwallon da ta dauka a bana rijista da ya hada da Robert Lewandowski da Raphinha.

Hakan ya biyo bayan da La Liga ta yi bincike don tabbatar da Barcelona na bin ka’idojin da aka gindaya a hukumance.

Hanyyoyin da kungiyar ta bi don fita daga kangin da take ciki sun hada da sayar da hannun jarin nuna wasanninta a talabijin a nan gaba, da cefanar da mallakar gabatar da shirye-shiryen a Barca Studios.

A cikin watan Agusta ta sayar da karin kaso 24.5 cikin 100 na Barca Studios ga Orpheus kan £84.6m, hakan ne ya sa tta samu isassun kudin yin rigistar wasu ‘yan wasan da ta dauka a kakar nan.

Baecelona tana mataki na biyu a teburin La Liga mai maki 16, bayan wasa shida da fara babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana da tazarar maki shida tsakaninta da Real Madrid mai jan ragama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *