Cire tallafin fetur: Buhari ya kare manufar gwamnati

Ayyukan raya kasa: Shugaba Buhari ya jinjna wa Ganduje

Shugaban Kasa Buhari

Tura wannan Sakon

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kare matakin da gwamnatinsa ta dauka na bijire wa shawarar hukumar bayar da lamuni ta Duniya watau IMF wajen cire tallafin man fetur a kasar.

Ya ce, halin da wadansu kasashe suka tsinci kansu a sakamakon cire tallafin, izina ce ga Nijeriya Yayin da yake amsa tambayoyi daga Jaridar Bloomberg, shugaban ya ce, su kansu manyan kasashen duniya da suka cire tallafin, yau suna yaba wa aya zakinta saboda illar da matakin da suka dauka ya haifar masu.

Buhari ya ce, gwamnatinsa a shekarar da ta wuce ta 2021, ta kaddamar da shirin cire tallafin, amma bayan tuntuba mai zurfi daga masu ruwa-da-tsaki, da kuma halin da ake ciki a wannan shekara ta 2022, daukar matakin cire tallafin ba zai haifar wa kasar da mai ido ba.

Ya ce, abin da ke gabansu shi ne, bunkasa hanyoyin samar da tataccen man fetur a cikin gida da kuma bai wa ‘yan kasuwa damar shiga harkar, domin damawa da su wajen kafa manya da kananan matatun mai kamar irin su kamfanin Dangote da BUA da Waltersmith.

Rahotanni sun ce, Nijeriya ta kashe akalla Naira triliyan hudu karkashin wannan gwamnati, wajen biyan tallafin man fetur domin ganin jama’ar kasar sun sayi man cikin sauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *