D/Tofa ta sami yabo saboda gina hanyar Babbar Ruga-Fango

Jabiru A Hassan Daga Kano
Al’umomin garuruwan Babbar Ruga zuwa Fango sun yaba wa majalisar kkaramar hukumar Dawakin Tofa bisa jagorancin Alhaji Ado Tambai Kwa saboda aikin hanyar su da ya ke yi wadda suka dade suna fatan ganin an samar da ita.
Wakilinmu wanda ya ziyarci garuruwan da hanyar ta ratsa, ya ruwaito cewa, aikin yana tafiya cikin nasara, sannan akwai alamun cewa, kamfanin da ke gudanar da aikin zai kammala ta kan ka’idar da aka yi duk da cewa, yanzu ana cikin yanayi na damina.
Gaskiya Tafi Kwabo ta zanta da wadansu mutane yayin da wakilinmu ke duba yadda aikin hanyar ke tafiya, inda dukkanin wadanda suka yi magana kan aikin hanyar suka bayyana jin dadinsu saboda ganin za’a samar da hanya mai kyau duba da yadda ake da garuruwa masu yawa masu amfani da hanyar.
Malam Adamu Chedi Babbar Ruga yace “ gaskiya idan aka kammala hanyar mun sami damar rubanya harkokinmu na sufuri tare da fito da kayan amfanin gonakinmu cikin nasara, domin haka muna godiya da shugaba Alhaji Ado Tambai Kwa bisa namijin kokarin da yake mana”. In ji shi.
A garin Fango, wakilinmu ya gana da Malam Jafaru direba wanda ya bayyana jindadi dangane da aikin hanyar, tare da jaddada cewa, majalisar karamar hukumar Dawakin Tofa ta yi masu komai duba da yadda aikin hanyar zai zamo alheri garesu, ya yi fatan cewa, al’ummar yankin za su ci gaba da bai wa karamar hukumar goyon baya da hadin kai.
A nasa bangaren, shugaba Ado Tambai Kwa ya shaida wa wakilinmu cewa, za su ci gaba da gudanar da ayyukan, domin ganin kowace mazaba ta amfani ribar dimokuradiyya tare da jaddada cewa, gwamnatinsa tana aiki ne bisa la’akari da bukatun al’ummar yankin, inda kuma ya gode wa gwamna Ganduje saboda kulawa ta musamman da yake bai wa kananan hukumomin jihar Kano.