Da’awah kan kashe wa gidan marayu Naira miliyan 12 -A duk shekara

Da’awah Orphanage

Da’awah Orphanage

Tura wannan Sakon

Danjuma Labiru Bolari Daga Gombe

Gidan marayu na Da’awah da ke unguwar Tumfure a jihar Gombe watau, Da’awah Orphanage, yana bukatar tallafin al’umma domin yanzu haka akan kashe Naira miliyon daya da dubu 15 a duk wata.

Shugaban kwamitin gudanarwa na gidan, Dokta Babayo Kolo, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda suke son gwamnati ta shigo domin bayar da gudumawa, kasancewar kudaden da ake kashewa ya yi yawa kuma samun tallafin ya yi kadan.

Babayo Kolo, ya ce, an bude gidan marayun ne da Marayu guda takwas a ranar 6 ga Fabarairu na shekara ta 2011, inda ya zuwa yanzu banda wadanda aka yaye, gidan yana da marayu 63. Ya ce, banda wannan, asalin gidan yana da marayu 1,750 a gidaje daban-daban guda 250 a cikin gari, wadanda suke a karkashin kulawarsu.

A cewarsa, kashi 100 na ciyar da marayun da karatunsu da duk wata dawainiya tana kansu, domin banda kananan yaran da manyan da suke matakin karatun sakandare suna makarantu masu zaman-kansu da kuma makarantun musaya da ake biya musu kudin makaranta.

Har ila yau, Dokta Kolo, ya kara da cewa, yadda gidan ke samun kudin gudanarwa, shi ne ma’aikatan gidan ke bayar da tallafi daga aljihunsu, sannan wasu daidaiku suke taimakawa.

Ya kuma yi amfani da wannan damar ya yi kira ga masu hannu-da-shuni da su shigo domin bayar da tasu gudummawar musamman wajen gina musu ajujuwan Islamiyya. A cikin masu taimakawa gidan wajen kudin da ake kashewa ya ce, “Bala Bello Tinka shi kadai ya dauki nauyin albashin gidan na Naira miliyon daya da dubu 600 na shekara” inji Kolo.

Da take karin haske, daya daga cikin ma’aikatan gidan, Da’awah kan kashe wa gidan marayu Naira miliyan 12 -A duk wata Zainab Adamu Abubakar, ta ce, suna bukatar gwamnati ta shigo wajen taimaka musu, musamman a bangaren kiwon lafiya da kuma abinci.

Zainab, ta ce, a wasu lokutan kungiyoyi masu zaman kansu watau NGOs da kuma daidaikun al’umma su ne suke tallafawa gidan da kayan abinci da tufafin yaran. Sannan ta ce, da gwamnati za ta shigo ta samar musu da koda karamin asibiti ne da za su ji dadi, saboda rashin lafiyar marayun.

Kiyasin kudaden da ake kashewa a gidan a shekara ya kai Naira miliyon 12, inda ake sayen ruwa da kayan abinci na fiye da Naira dubu 600 a wata.

Ta kara da cewa, a shekara ana kashe Naira miliyon bakwai da dubu 284 a bangaren karatu da Naira miliyon biyu da dubu 331 a bangaren kiwon lafiya da dubu 630, a bangaren albashi da kuma Naira miliyon daya da dubu 642 a kan kananan gyaregyare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *