Da’awar kin biyan kudin dako: IPMAN ba ta yi adalci ba –Injiniya Farouk

Farouk Ahmed

Tura wannan Sakon

Hukumar kula da sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur, NMDPRA, ta ce, ikirarin da kungiyar dillalan man fetur, IPMAN, ta yi cewa, ba a biyan su kudaden dako ba gaskiya ba ne.

Tun da farko, dillalan man fetur sun fara yajin aikin gargadi na kwana uku daga Litinin da ta gabata, saboda zargin kin biyan su kudaden. A tattaunawarsa da manema labarai, shugaban hukumar NMDPRA,

Injiniya Farouk Ahmed, ya ce daga watan Disamba bara zuwa watan jiya sun biya mambobin kungiyar kudin dakon mai fiye da Naira biliyan 100.

Injiniya Farouk ya ce, babu watan da suke fashin biyan dilalan man kudadensu, domin haka idan aka ce ba sa biya, wane ne ake bai wa kudaden Ya ce, sun sha zama da shugabanni da mambobin IPMAN kan batun biyan su kudadensu na mai, kuma suna cika alkawura.

Har ila yau, ya ce, bayan korafin cewa, ana zaben masu ido-da-kwalli wajen biyan kudaden, ya sa suka dauki matakin soma biyan kananan masu dillalai, ko a watan Agusta a cewarsa sun biya Naira biliyan 20.

Farouk ya ce, batun an yi wata takwas ba a biya wani ba, ba gaskiya ba ne, domin tsari suke bi kan jadawali na musamman da suke amfani da shi wajen bai wa mutane kudadensu. A cewarsa, “idan za a fadi gaskiya a fadi, idan an yi kuskure a fadi kuskure”.

Injiniya Farouk ya kuma kara da cewa, idan ma an samu jinkiri to laifi ba daga garesu ba ne.

Saboda su ma akwai inda sai sun karbo kudaden sannan za su biya, domin haka duk kudin da ya shiga hannusu suna fitarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *