Dabbobi sun yi sauki a kasuwannin Kano –Rahoto

Dabbobi sun yi sauki a kasuwannin Kano –Rahoto

Dabbobi sun yi sauki a kasuwannin Kano

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Farashin dabbobi da nau’in tsuntsaye yayi kasa a mafiya yawan Kasuwannin kauyuka da guraren sayar da dabbobi a fadin jihar Kano, inda wakilin mubya ruwaito cewa dabbobi nau’in raguna da tumaki da awaki da shanu da kuma rakuma sunyi kasa inda ake samun rangwamen farashi fiye da makonni 3 Zuwa 4 da suka gabata.

A kasuwar Badume dake yankin Karamar hukumar Bichi, wadda kuma take ci ranakun Lahadi da Katana, an sayar da manyan raguna daga dubu 50-100, sai matsakaita da aka sayar 30-40, sai awaki da tumaki aka sayar daga dubu 25-35 yayin da aka sayar da kaji da agwagi da talo-talo da zabi kan kudi daga dubu 2-6.

Malam Abdullahi Maigata wani masani kan harkokin dabbobi kuma mai saye da sayarwa yace ‘ babu shakka dabbobi sunyi sauki sosai domin a makonni 3 zuwa 4 sun fi tsada don haka zan iya cewa an sami rangwamen farashi na dabbobi a wannan babbar Sallah, amma kuma duk da haka anyi cikini sosai mutane sun yi kokari”.

Inji shi A sauran guraren sayar da manyan dabbobi kamar Kofar Na’isa da kasuwar Dambatta da Wudil da kuma Getso,wakilin mu ya ruwaito cewa an sayar da babban Sa kan kudi naira dubu 250-300, matsakaita naira dubu 150-200, sai Kanana kan kudi naira dubu 55-70 kuma anyi ciniki sosai duk da jinkirin biyan albashi da aka samu.

Haka kuma mafiya yawan dillalan dabbobi da wakilin namu ya tattauna dasu sun nunar da cewa duk da rashin kudin da ake fama dashi, mutane sunyi kokari kwarai da gaske wajen sayen raguna da shanu da kuma kaji har ma da wadanda suka sayi rakuma sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *