Dakile tono fetur: Kwamitin gano shafaffu da mai ya kama aiki

Babagana Monguno
Daga Mahmud Gambo Sani
Gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti mai mutane 11 da zai gudanar da bincike kan zarge-zargen satar man da ake yi wa shafaffu da mai da jami’an tsaro, abin da ke sanya Nijeriya kasa fitar da man da take bukata.
Mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Janar Babagana Monguno shi ya kaddamar da kwamitin, a karkashin tsohon janar na sojin Nijeriya, Barry Ndiomu, yayin da Dabid Attah zai zamaSakatare.
Janar Monguno ya ce, abin takaici ne ganin yadda Nijeriya ke tafka asarar maaudan kudade saboda yadda ta’annatin barayin mai ya yi karfi, kuma suke cin amanar kasa wajen sace danyen man da kasar ta dogara da shi wajen samun kudaden shiga.
Ya danganta satar man da yaddda kasar take asarar kudaden shigar da ta saba samu, wadanda ake gudanar da ayyukan raya kasa da su.
Monguno ya kuma ce, abin takaici ne yadda a halin yanzu ake shan wahala wajen samar da ganga miliyan guda kowace rana, sabanin ganga miliyan guda da dubu 800 da kungiyar kasashe masu arzikin mai na OPEC ta ba ta damar fitarwa.
Jami’in ya ce, ya zama wajibi a gudanar da bincike domin gano masu hannu a ciki da wadanda ake hada baki da su, ciki har da jami’an tsaro da kamfanonin kasashen ketare domin daukar mataki mai gauni a kai.