Dalibai 500 sun sami gurabe a makarantar Kimiyar Lafiya -In ji Shugaban Makarantar

Dokta Bello Dalhatu
Daga Alhussain Suleiman
Sababbin dalibai da suka hada maza da mata makarantar kimiyar lafiya da fasaha ta jihar Kano, ta dauka a wannanshekara 2021 zuwa 2022 da za su karanci fannoni daban-daban a kan harkokin lafiya ta yadda idan suka kammala cikin nasara za su taimaka wa al’ummar jihar da ma kasa baki daya da yardar Allah.
Bayani ya fito ne daga bakin shugaban makarantar, Dokta Bello Dalhatu a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin shi da ke makarantar,
Doktan ya yi kira ga sabbin daliban da suka samu nasarar fara karatun da su za ma jakadu na gari abin koyi tare da mayar da hankulan su a kan karatu domin karatun lafiya ba’a batun daga kafa duk abin da dalibi ya aikata shi zai taras.
Ta bangaran malamai kuwa Malam Bello Dalhatu ya tabbatar da cewa, makarantar ta na da kwararrun malamai masu hazaka da kwarewa a kan fannonin da suka karanta.
Duk da malaman da suke da su gwamnatin jihar Kano a karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya na matukar kokari, wajen ganin makarantun koyon aikin lafiya sun zauna daram a fadin jihar, domin duk abin da suke bukata gwamnatin ta Ganduje ta na ba su ba tare da bata lokaci ba in ji Kwamared Bello Dalhatu.
Zuwa yanzu makarantar tana da adadin malamai da yawansu ya kai 126, sai ya yi amfani da wannan dama da gode wa gwamnan jihar da kwamishinan lafiya na jihar, a kan kokarin da suke yi wajen kara inganta harkokin lafiya a daukacin jihar, ya ce, babu shakka kwamishinan ya rike amanar gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Daga karshe, ya ce, makarantar ta kai wani matsayi da za ta iya gogayya da sauran makarantun kiyon lafiya da ake da su a fadin Arewacin Jijeriya wannan ya samu ne a bisa jajircewar gwamnan jihar da kwamishinan lafiya