Daliban jami’o’i, a jajirce kan manufa -Shugaban Madaba’ar Triumph

Shugaban Madaba’ar Triumph
Daga Mahmud Gambo Sani
Shugaban madaba’ar jaridun Triumph, Malam Lawal Sabo Ibrahim ya hori ‘yan kungiyar zaburar da dalibai a kan kishin kasa da sana’o’in dogaro da kai mai suna Think Big Association da su himmatu wajen mayar da hankali kan karatunsu domin su zama manyan da za a yi alfahari da su a nan gaba.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a lokacin da ‘yan kungiyar suka kai masa ziyarar girmamawa da kuma godiya a ofishinsa bisa gudummawar da madaba’ar take ba su wajen yada manufofin kungiyar a kafofin sadarwarta.
Malam Lawal Sabo ya kuma jawo hankalinsu da su tsaya su tantance da tsara kungiyar bisa ka’ida, inda ya kara da cewa, “harkar kungiya abu ne da ya kamata mutum ya tsaya ya nutsu wajen tantance irin mutanen da ya kamata ku yi mu’amala da su, domin gudun fadawa mu’amula da mutanen da ba su kamata ba.”
Ya kara da cewa, “kowace kungiya tana da manufa da kuma burin da take so ta cim ma domin samar da ci gaba a tsakanin al’umma.” Daga bisani ya yi kira ga ‘yan kungiyar da su yi kokari wajen samar wa da kungiyarsu hanyoyin samun kudin shiga domin tabbatar da dorewar tafiyar.
A karshe ya yi alkawarin taimaka wa kungiyar a kowane lokaci wajen ganin ta sami nasarar da ake bukata.
Tun da farko da yake jawabi, shugaban kungiyar Umar Hassan Abubakar ya ce, sun kirkiri kungiyar domin zaburar da ‘yan uwansu dalibai a kan saka kishin kasa a zukatansu da kuma riko da sana’o’i domin dogaro da kai.
Ya ce, “A lokacin da aka sami vullar annobar Korona, dalibai sun zauna kusan shekara daya a gida babu karatu, sai muka ga ya kamata mu yi amfani da wannan damar wajen wayar da kan ‘yan uwanmu da su rungumi sana’o’i domin dogaro da kai.”
Da yake jawabi, Editan kungiyar Musa Umar ya ce, kungiyar a halin yanzu tana da mambobi daga manyan makarantun da ke fadin jihar Kano, inda suke shirye-shiryensu