Daliban Kano sai tsalle: Gwamna ya biya wa kowannensu kudin jarrabawar NECO

Tura wannan Sakon

Fassara Aliyu Umar

A ranar Litinin da ta gabata,gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje,ya amince da sakin Naira miliyan 104.3 domin biyan Majalisar kula da jarrabawa ta kasa(NEC) kudaden da daliban jihar suka rubuta.

A wata takardar bayani da ke dauke da sanya hannun babban sakataren yada labarai na gwamnan,Malam Abba Anwar,ta bayyana cewa,tuni Majalisar kula da jarrabawar Sakandare ta kasa ta yi na’am da shigar kudin cikin asusunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *