Dan majalisa ya kaddamar da titin ‘Yan Alewa-Kwanar Diso

Alhaji Lawan Abdullahi Kenken

Alhaji Lawan Abdullahi Kenken

Tura wannan Sakon

Daga Habibullahi Ibrahim Abdullahi

A ranar Talatar da ta gabata, dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukuma Gwale, Alhaji Lawan Abdullahi Kenken ya kaddamar da aikin titi Gwale ‘Yan Alewa zuwa kwanar Diso.

A lokacin kaddamar da karashen aikin, kamar yadda al’ummar unguwar suka nema, wanda dama tuni ya yi aikin inda ya fara daga kwanar Diso zuwa ‘yan Alewa, domin haka ya amsa kiransu, kuma na take ya bayar da umarnin fara aikin.

Wakilin mutanan Gwale da ya ke gabatar da jawabinsa a yayin kaddamarwar, bayan ya yi godiya ga Allah, ya yi kira ga mutanan yankin da aikin ya shafa da su bai wa ’yan kwangilar aikin hadin kai, domin samun nasarar aikin.

Haka kuma ya yi kira gamasu kula aikin da cewa, lalai su tsaya su tabbatar an yi aiki mai kyau, wanda za a dade ana mora.

Daga karshe, wakilinmu ya kara da cewa, akwai tituna da dama da yake kwana yake tashi da su a cikin ransa, wanda kuma tuni ya yi rubutu a kansu ya tura, sai dai at aya da addu’ar Allah ya cika mana wannan fata na mu.

Titunan wadanda suka hadar da titin Dorayi wanda ya tabbatar da cewa, idan Allah ya yarda za a fara aikinsa a kusa, duba da yadda mazauna gurin suke shan wahala.

Titin Kofar Waika zuwa Dabai sai titin da ya tashi daga gidan Sheikh Uba Sufyan duka wadannan idan Allah ya yarda za mu yi duk mai yiwuwa muga an yi su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *