danganta matsalolin Nijeriya da rashin ilimi

danganta matsalolin Nijeriya da rashin ilimi

Sule Musa Kadawa

Tura wannan Sakon

Labari daga Ibrahim Muhammad Kano

Sule Musa Kadawa Dan takarar maja­lisar jahar Kano na karamar hukumar Ungogo daga jam’iyyar PDP.Yace ilimi shine gishirin zaman Duniya kuma jam’iyyar su ta PDP tayi abubuwa da yawa a baya na inganta il­imi tun daga kan na addini dana zamani har makaran­tun manya akayi a kauyu­ka dana yaran Fulani.

Yayi nuni da cewa irin matsaloli da aka shiga a kasarnan yanada dangan­taka da rashin ilimi kuma su a Ungogo an sami gaza­wa a wakilci abubuwan ili­mi ya tab arb are makarantu ba wajen zaman yara ba makewayi ba karin gine-gine na ajujuwa yanzu karatunma na Neman ya gagari dan talaka.

Yace in Allah ya basu nasara za’a tabbatar il­imi ya samu dan talaka yayi karatu cikin sauki da walwala.Yanzu takai dan talaka ba zai iya kara­tu ba,Hatta masu mulki ya’yansu basa karatu a makarantun Gwamnati sai masu zaman Kansu saboda ba’a basu kulawa.

Suke Kadawa yace in sukaci sab e ba b angaren ilimi kadai ba duk wani b angare na rayuwa da musammam b angaren za­man lafiya zasu kyautata tsaro a kauda duk abubuwa dake hana mutane su wal­wala komai zai daidaita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *