Dattawan Arewacin Yobe, sun yi na’am da takarar Machina

Bashir Machina
Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
A kokarin da shugaban majalisar dattawan kasar nan, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan ke yi domin samun tikitin tsayawa takarar komawa kujerarsa a majalisar kasa, karkashin jam’iyyar APC daga mazabarsa ta Arewacin jihar Yobe, sai dakushewa yake yi tare da canza salo, musamman ganin cewa, wasu masu ruwa-datsaki na jam’iyyar APC a mazabar na nuna goyon bayansu ga takarar Alhaji Bashir Machina, a zaben da ke tafe na 2023 domin maye gurbin Sanata Ahmed Lawan.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar goyon bayan takarar Alhaji Bashir Machina, Malam Abba Maina Yusufari, da aka raba wa manema labarai a garin Damaturu, ya ce, “Muna son mu nuna karfin gwiwa wajen nuna goyon bayanmu ga dan uwanmu, Alhaji Bashir Sheriff Machi- na, domin ya karbi ragamar mulki daga hannun Sanata Ahmed Lawan a shekarar 2023”.
“Kamar yadda kuka sani, Alhaji Bashir Machina ne dan takarar da aka zaba a matsayin dan takarar babbar jam’iyyarmu ta APC a zaben fid da gwani da aka kamala”.
“Don haka, duk wani yunkuri da Sanata Ahmed Lawan zai yi na maye gurbinsa daga kujerarsa, zai zama cin amanar al’umma ne da kuma cusa turbar rashin zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’ummomin yankinmu na shiyyar Yobe ta Arewa.”
Ya kara da cewa “wannan yunkuri na tsayawa takarar Alhaji Bashir Machina, aikin mutane ne ba na mutum daya ba, don haka, muna so a yi taka-tsantsan cewa, yunkurin toshe muryar jama’a da kowane mutum zai so ya yi ko dai ta hanyar sa hannu a cikin wani nau’i na makirci, zai zama cin karo da manufar dimokuradiyya da adalci.”
“Mun shirya yin aiki tukuru domin ganin mun cim ma nasarar dan takararmu da kuma nasarar jam’iyyarmu a dukkan matakai”.
“Muna kira ga dan uwanmu, Dokta Ahmed Lawan, da ya mika godiyarsa ga mutanensa kan irin goyon bayan da ya samu daga wajensu tun bayan dawowa mulkin dimokuradiyya a Nijeriya a shekarar 1999, bisa ga yadda a kowane lokaci musamman yayin zabe suke goya masa baya.”
Idan ba a manta ba, shugaban majalisar ta dattawa, Sanata Ahmed Lawal, a kwanakin baya ya tsaya domin a fafata da shi a takarar neman kujerar shugabancin kasa wanda Bola Ahmed Tinubu ya kayar da shi da sauran ‘yan takara, wanda hakan ya sa shi shiga halin nan na jifan gafiyar Bedu