Dattawan Diso sun ziyarci shugaban karamar hukumar Gwale

Dattawan Diso sun ziyarci shugaban karamar hukumar Gwale

Dokta Khalid Ishak Diso

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

A ranar laraba da ta gabata 24 ga watan Nuwanba 2021, dattawan cigaban unguwar diso da kewaye sun ziyarci shugaban karamar hukumar gwale inda suka tattauna abubuwa masu mahimmanci ga rayuwar alummar wannan karamar hukumar wanda suka hada da samar da harkar tsaro, aikin yi ga matasa maza da mata, aiyukan raya kasa da kuma sauransu.

Da yake jawabi a wajen ziyara mai unguwar diso Ahmed Bello yace wannan shi ne ziyara ta farko a tarihin wannan karamar hukuma kuma ya bayyana godiya ga Allah madaukakin sarki da ya aramana wannan rana ta ganin wannan ziyara ta tabbata.

 Mai unguwar yayi addu`a da cewa yadda aka fara wannan taro lafiya Allah yasa a gama lafiya.

Ana sa jawabin jagoran dattawan cigaban unguwar diso da kewaye Alhaji Umaru Maje Diso, ya jinjinawa shugaban karamar hukuma gwale Dokta Khalid Ishak Diso saboda jajircewarsa wajen samar da aiyukan raya kasa da cigaban alumma.

Yace karamar hukumar gwale na daya daga cikin kananan hukumomi da aka kirkiro a zamanin shugaban kasa janar Sani Abacha yakuma bayyana irin  gwagwarmaya da akayi Kafin ta tabbata. Ya kara da cewa wannan karamar hukuma Allah ya albarkace ta da hazikan mutane musammam yan boko, malaman addini, yan kasuwa, da ma`aikatan gwamnati. Amma abun takaicin a nan shine har yau karamar hukumar gwale itace koma baya wajen samar da ma`aikata a kananan hukumomin a wannan jiha.

 Umaru ya bayyan cewa harkar tsaro wani bangare ne dake da mahimmanci a ko wacce irin alumma a fadin duniyar nan. Domin sai da tsaro jama`a ke cigaba da bunkasar tattalin arzikin kasa don haka akwai bukatar kara kaimi da tashi tsaye domin ganin an karfafa harkar tsaro a wannan karamar hukuma.

 Maje ya kara da cewa harkar ilimi wani bangare ne mai zaman kansa domin  duk alummar da bata da ilimi tabbas babu cigaba don haka ilimi shine gishirin zaman duniya kuma shine sinadarin rayuwa. Dukkan ruhin da aka gina batare da ilimi ba laile za`a samu nakasu a gareshi, tasirin ilimi ya kunshi abubuwa mai yawa kamar, gyaran rayuwar alumma, samar da nagartattun mutane, zama cikin aminchi batare da tashin hankali ba, samar da arziki da sauransu, don haka wannan yasa dole mu yaba wa shugaban karamar hukumar gwale wajen ganin gwale ta cigaba da rike kanbunta na ilimi da kuma bawa harkar mahimmanci sai dai akwai wasu makarantun da suke bukatar kulawa musamman ta wajen gyara da kuma samar da kujeru da gyara katangu domin hana yan bata gari haurawa cikin makaranta.

Mal Umaru ya kuma kira ga shugaban karamar hukumar da ya cigaba da aiyukan raya kasa da ya fara domin cigaban alummar wannan karamar hukuma da kuma samar da hanyar ruwa ta zamani domin a gari kamar birnin kano amfani da bulo ya zama tsohon yayi ana maganar kankare ko zubi kawai domin inganci.

Shi kuma ana sa jawabin tsohon ma`aikacin motsa jiki da wasanni na jami`ar  Bayero kano kuma daya daga cikin dattawan unguwar diso Alhaji Isyaku yayi kira ga karamar hukumar data kafa  kwamiti na tsofaffin ma`aikatan gwamnati musamman tarayya domin ganin matasan wannan karamar hukuma ba a barsu a baya ba wajen samar da aiyuka ga matasa daka gwamnatin tarayya.

Ya kuma ce ya kamata wannan karamar hukuma ta karrama Dokta Hassan Suleiman saboda jajircewarsa da kokarinsa wajen samawa yan wannan karamar hukuma aiki daka gwamnatin tarayya.

Shafi`I Umar ma`aikaci a asibitin Aminu Kano ya kira ga karamar hukuma data dinga amfani da blue print ko debelopment plan domin wannan zai temaka kwarai da gaske wajen aiyukan cigaba na yau da kullum ga karamar hukuma.

Ya kuma shawurci karamar hukuma da ta samar da wani yanayi wajen kokarin ganin ta hada taro da ake kira Summit a karamar hukuma ba shakka wannan zai temaka wajen bayar da shawarwari da kuma cigaban karamar hukuma.

Muhammad Ahmad Diso wanda kuma tsohon ma`aikacin hukumar NDE ne ya yaba shugaban karamar hukuma wajen kokarin da ya keyi domin cigaban wannan unguwa kuma ya jinjina masa saboda nada Baffa Audu Diso wanda ya fito da ga wannan mazaba a matsayin daya da cikin masu bashi shawara a wannan karamar hukuma.

Ana sa jawabin mai gayya mai aiki shugaban karamar hukumar Dokta Khalid Ishak Diso ya bayyana godiyarsa da farin cikin sa dan gane da wannan ziyara da kuma bayarda shawarwari domin cigaban alummar wannan karamar hukuma.

Yace babu wata gwamnati ko hukuma da zata cigaba idan har alummar ta basu gamsu da yadda ake gudanar da mulki ba don haka wannan ziyara ta nuna a fili cewa alummar unguwar diso sun gamsu da irin aiyukan da karamar hukumar gwale take yi a yanzu. Ya kara da cewa gudunmawar alumma da bayar da shawarwari shi ke kawo cigaban gwamnati da kuma bunkasa tattallin arzikin kasa. Yace babban kalubale da wannan karamar hukumar take fuskanta a yanzu shine matsalar samar da kudaden shigowa ba shakka babu wata gwamnati ko hukuma da zata samu cigaba musamman wajen aiyukan raya kasa da walwalar jama`a idan har bata da hanyar shigowar kudade wato (rebenue) don haka wannan karamar hukuma ta dukufa ka`in da na`in wajen samar da hanyoyin kudaden shiga domin aiyukan alheri da kuma cigaban alumma.

Shugaban yace karamar hukumar gwale ta dauki ma`akatan lafiya wanda suka gama karatu na lafiya kuma suke aiki a wannan karamar hukuma sama da shekara 20 batare da albashi  ba yanzu haka sun zama ma`aikata na din din din wato permanent wanda za`a dugga basu albashi na 20,000 duk wata.

Ya kara da cewa a yanzu haka akwai yan gwale da dama wanda wannan karamar hukuma ta samawa aiki a ma`aikatu daban daban wanda suka hada da hukumar karota, aikin dan sanda, aikin cibil defence da kuma aikin soja kuma duk wannan mazabu goma na wannan karamar hukuma babu inda bamu gudanar da aiyukan raya kasa ba domin cigaban alumma.Ya Bayyana cewa akwai makarantu guda biyar sababbi da wannan karamar hukuma ta gina don bunkasa harkar ilimi musamman ilimin islamiyya domin duk yaron da ya samu hardar karatun al kur`ani zaka ga cewa karatun boko ya zama mai sauki a gurinsa.

Shugaban ya bayyana cewa karamar hukumar gwale ta dauki matakai daban daban wajen ganin harkar tsaro ta inganta domin tsaro wani bangare ne mai zaman kansa sanin kowa ne cewa duk alummar da ba tsaro babu zaman lafiya da kwanciyar hankali da cigaban alumma don haka wannan karamar hukuma ta bawa tsaro mahimmanci kwarai da gaske.

Baffa Audu Diso wanda shine mai bawa shugaban karamar hukumar gwale shawara ta fuskar siyasa ya nuna farin cikin sa da godiyarsa dan gane da wannan ziyara mai mahimmanci wadda itace ta farko a tarihin wannan unguwar diso da kewaye ya kuma ya bawa shugaban karamar hukumar saboda kulawa da yake yiwa wannan mazaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *