Daurin aure: Dambazau ya yi wa mahalarta ban-gajiya

Dambazau

Dambazau

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

Dan majalisa mai wakiltar Takai da Sumaila a majalisar tarayya da ke Abuja, Shamsuddeeni Abdurrahman Danbazau ya mika sakon ban gajiya ga al’umma bisa halartar daurin auren kanwarsa da aka yi ranar Asabar da ta gabata.

Ya yi godiya ga ‘yan Nijeriya wadanda suka halarci daurin auren wanda kuma suka zo daga dukkannin jihohin kasar nan duk da irin harkokin da ke gabansu domin sai da bikin wanda haka ya tabbatar da cewa, ‘yan Nijeriya mutane ne masu hadin kai da kaunar juna.

Daga karshe, ya yi godiya ga dukkan wadanda suka halarci daurin aure da fatan kowa ya koma gidansa lafiya. Ya ce, a matsayina na dan majalisar Takai da Sumaila a majalisar tarayya zan ci gaba da ganin cewa, duk wani abu da zai kawo ci gaban al’ummar mazabarsa Daurin aure: Dambazau ya yi wa mahalarta ban-gajiya ya sanar da shi.

Ya kara da cewa, daga hawansa zuwa yanzu ya samu nasarori daban-daban musamman wajen samar da aikin ga matasa maza da mata da kuma tallafi wajen ci gaban harkar ilimi da makamantansu. Ya kuma gode wa al’ummar mazabar Takai da Sumaila saboda goyon baya da suke ba shi wajen samar da romon dimukaradiyya.

A nasa jawabin, shugaban manoman Takai, Alhaji Yakubu Ibrahim Tagahu ya yi wa ma`auratan fatan alheri da kuma zaman lafiya domin shi aure abu ne na din-din-din dole sai an hada da hakuri domin duk inda kaji an ce hakuri dole wani sai an bata masa.

Shugaban manoman ya yi kira ga ma`auratan da su zauna lafiya da kuma rike dokokin aure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *