Depay, ka san inda dare ya yi maka –Barca

Mai horas da ‘yan wasan Barcelona Dabi ya fada wa dan wasan gaba na Netherlands Memphis Depay cewa ya san na yi bayan da kungiyar ta dauko Robert Lewandowski daga Munich, da kuma dan wasan Brazil dinnan Raphinha, mai shekara 25. (AS – in Spanish)
Sai dai ana cewa Ronaldo zai shaida wa Manchester United din cewar zai bar kungiyar, kuma ba zai karbi tayin da za su masa ba. (Sun)
Aniyar kungiyar Chelsea ta daukar dan wasan baya na Seb illa Jules Kounde na cikin hadarin rushewa ganin cewar Barcelona na kara kaimin ganin ta dauki dan wasan na Faransa mai shekara 23. (Guardian)
Idan har Chelsea ba ta samu nasarar dauko Kounde ba, to za ta fara tunanin sayo dan wasan B illarreal Pau Torres mai shekara 25, ko Milan Skriniar na Inter Milan da kuma matashin dan wasannan dan asalin Croatia Josko Gb ardiol wanda yanzu ke wasa a RB Leipzig. (90 Min)
Chelsea ta yi tayin bayar da dan wasanta Timo Werner, ga RB Leipzig a kokarinta na shan gaban Paris St- Germain wajen sayen dan wasan baya na Faransa Nordi Mukiele mai shekaru 24, daga kungiyar, mai buga gasar Bundesliga. (Foot Mercato, b ia Metro)
Dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo zai tafi Ingila domin tattaunawa da Manchester United kan makomarsa a kungiyar. (Athletic)
West Ham ta kammala cimma yarjejeniya da dan wasan gaba na Italiya Gianluca Scamacca, kuma ana sa ran za a duba lafiyarsa a yau Talata gabanin kammala dauko shi daga kungiyar Sassuolo. (Guardian)
AC Milan na tunanin kara kudi kan tayin da suka yi na sayen dan wasan tsakiya na Club Bruges Charles de Ketelaere, wanda ake alakantawa da kungiyar Leeds United, domin ganin ko cinikin nata zai fada. (Calciomercato – in Italian)
AC Milan kuwa na shinshinar dan wasan gefe na kungiyar Chelsea Hakim Ziyech kuma dan wasan mai shekara 29 dan asalin kasar Morocco na son komawa kungiyar wadda ke taka leda a gasar Serie A. (Calciomercato – in Italian)
Lyon ta ce a shirye take ta saurari tayin da za a yi wa dan wasanta mai shekara 24 dan asalin kasar Brazil Lucas Pakueta, wanda ake alakantawa da kungiyar Arsenal. (Metro)
Dan wasan gaba na Najeriya B ictor Osimhen, ya ce duk wani batu na sauya shekarsa jita-jita ce kawai domin kuwa shi yana jin dadin zamansa a Napoli. (Corriere dello Sport – in Italian)