Digirgiren tattalin arziki: Tilas Nijeriya ta cire tallafin mai -Zainab Shamsuna

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Gwmnatin tarayyar ta ce, ta yi nasarar janye tallafin hasken lantarki ba tare da an sani ba, kuma janye tallafin man fetur ne abin da za ta yi nan gaba.

Ministar kudi da tsare-tsare, Hajiya Zainab Ahmed Shamsuna ce ta bayyana haka a wani taron ministocin kudi na kasashen Afrika da asusun bayar da lamuni na duniya. Ta ce, annobar korona da kuma babban zaben kasa mai zuwa ne ma ya kawo cikas a game da janye tallafin mai.

Ministar ta ce, tallafin man fetur ne ya zame wa gwamnatin Nijeriya babbar matsala, inda ta kara da cewa, tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya zai dada tsananta al’amura. Ta bayyana fatan samun amincewar majalisar dokokin kasa domin ci gaba da shirin gwamnati na janye tallafin man fetur gaba daya.

.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *