Doguwa ya albarkaci saukar Alkur’ani a AFCS

Alhassan Ado Doguwa

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

A ranar Asabar 6 ga watan Agusta shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta tarayya kuma wakilin kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa, Alhaji Alhassan Ado Doguwa ya kasance babban bako a wajen saukar Alkur’ani na makarantar sakandaren sojojin sama da ke garin Kwa watau (AFCS).

A cikin jawabin da ya gabatar wajen bikin saukar karatun, Doguwa ya ce, ya kasance wajen bikin domin shaida yadda dalibai makaranta suke samun ilimin addini da kuma yadda sashen Islamiyya na makarantar yake bayar da darussa da Doguwa ya albarkaci saukar Alkur’ani a AFCS kuma tarbiyya ga yara masu tasowa.

Ya ce “ Na taso daga Abuja ne musamman domin in shaida wannan sauka ta Alkur’ani kuma in hadu da makaranta da yadda suka koyi karatun ganin cewa, samun ilimi tun daga tushe abu ne mai kyau musamman ga yara kanana a wannan lokaci da duniya take tafiya a doron ilimi”.

Alhaji Alhassan Ado Doguwa ya hori wadanda suka sauke Alkur’ani da su yi amfani da ilimin da ke cikinsa wajen gina kasa da kuma bunkasa tarbiyya a duk inda suka tsinci kansu, tare da yaba wa shugaban makarantar, Wing Kwamanda M.Garba da daukacin malamai saboda kokarin koyarwa da suke yi ba tare da gajiyawa ba.

A karshe, shugaban masu rinjayen ya bai wa dalibai 5 da suka haddace Alwur’ani kyautar Naira dubu 100 kowannensu, sannan ya bayar da gudummawar Naira miliyan 1 ga kungiyar iyaye da malamai ta makarantar domin gudanar da wasdanu ayyukanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *